Aisha Buhari: Abin da ya sa take neman ƴan sanda su saki ma’aikatanta

Aisha Buhari

Asalin hoton, @amuhammadubuhari

Mai ɗakin Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi kira ga babban sufeto janar na Najeriya ya saki wasu ma'aikatanta da ake tsare da su.

Uwar gidan shugaban na Najeriya ta yi kiran ne ga babban sufeto janar na ƴan sandan a wani saƙon da ta wallafa a Twitter, inda ta ce tana son a saki jami'an ne don kauce wa jefa rayuwarsu a cikin hatsarin kamuwa da cutar korona a yayin da ake tsare da su.

Rahotanni sun ce ana tsare ne da babban dogarin uwar gidan shugaban da kuma wasu jami'an tsaron da ke bata kariya.

Kuma a jerin sakwannin da Aisha Buhari ta wallafa ba ta bayyana dalilin da ya sa ake tsare da su ba, amma wasu rahotanni sun ce an tsare su ne saboda sa'insa da wani mataimaki ga shugaban kasa.

Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga ofishin sufeto janar na ƴan sanda kan umurnin uwar gidan shugaban na Najeriya.

A jerin sakwannin da ta wallafa a Twitter, Aisha Buhari ta yi jan hankali ga hukumomin gwamnati su tabbatar da dokar kulle da shugaba Buhari ya sanya wa hannu tare da hukunta duk wanda ya saba wa dokar ta hanyar killace shi tsawon mako biyu.