IS ta yi ikirarin kashe mayaƙan sa-kai 90 a Borno

Mayakan ISWAP

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar IS da ke iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin kashe mayaƙan sa-kai 90 a jihar Borno yankin arewa maso gabashi.

A sanarwar da ta wallafa ranar Juma'a, IS ta ce mayaƙanta ne suka kai wa gangamin mayaƙan sa-kai hari a garin Gubio inda suka yi musayar wuta da ya kai ga kashe kusan 90 da raunana wasu.

Ta kuma yi ƙirarin cewa mayaƙanta sun yi ƙoƙarin kashe mayaƙanta bayan sun nemi su juya wa sojojin Najeriya baya.

Tun da farko rahotanni sun ce mutum 81 aka kashe a harin da aka kai ƙauyen Foduma kolamaiya da ke ƙaramar hukumar gubio a ranar Talatar da ta gabata.

Shugaba Buhari ya bayyana kaɗuwarsa da harin da aka kai Gubio tare da jajantawa al'ummar Borno da iyalan waɗanda aka kashe.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta