Rikicin Obaseki da Oshiomole: Yaushe za a kawo karshen siyasar ubangida a Najeriya?

..

Matakin da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dauka na hana Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo tsayawa takarar fidda gwani don fafatawa a zaben da za a yi cikin watan Satumba ya sake fito da ɓarakar da ke tsakaninsa da ubangidansa na siyasa Mista Adams Oshiomhole.

Mista Oshiomhole wanda shi ne shugaban APC na ƙasa, kuma tsohon gwamnan jihar ta Edo, ya taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen Mista Obaseki karo na farko a muƙamin gwamna cikin 2016.

Sai dai wani rikicin siyasa da ya ɓarke a tsakaninsu, wanda masu lura da lamura suke ganin ba shi da alaƙa da ƙoƙarin inganta rayuwar mazauna jihar, ya kai ga hana gwamnan sake tsaya wa jam'iyyar takara karo na biyu bayan da ta ce takardun karatunsa na bogi ne.

Ko da yake, Gwamna Obaseki ya ce ba zai roƙi jam'iyyar ta sauya matsayarta ba, lamarin da masu nazari kan harkokin siyasa ke ganin alama ce da ke nuna cewa gwamnan yana iya sauya sheƙa zuwa wata jam'iyyar.

Inda zai buƙaci ta tsayar da shi takara, kuma hakan ka iya jefa APC cikin ƙarin matsala idan manyan 'yan jam'iyyar ciki har da Shugaba Muhammadu Buhari ba su yi sulhu kan lamarin ba.

Wannan rikici na Mista Obaseki da Mista Oshiomhole ya sake bankaɗo irin mummunan tasirin da siyasar ubangida take yi kan mulkin dimokradiyyar Najeriya.

Masu sharhi a kan harkokin siyasa irin su Dakta Abubakar Kari na Jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa hana Mista Obaseki tsayawa takara a APC ya ƙara fito da illar siyasar ubangida a fili kuma hakan ba zai haifa wa dukkan bangarorin alheri ba.

"Hakan ya nuna cewa batun nan na ubangida ya yi kamari... (Gwamnan) yana da zaɓi guda biyu: na farko zai iya komawa wata jam'iyya...Na biyu yana iya zama a APC ya zamar mata ƙadangaren bakin tulu."

Mun yi wa Kwankwaso ritaya a siyasa

Asalin hoton, KANO GOVERNMENT HOUSE

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu daga cikin manyan rikice-rikicen da siyasar ubangida ta haifar sun haɗa da wanda ya faru tsakanin tsohon Gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu da tsohon Gwamna Akinwunmi Ambode; da tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da tsohon amininsa na siyasa Abdullahi Umar Ganduje, da makamantansu.

Misali, tun bayan zaben 2015 wanda Sanata Kwankwaso ya yi ruwa da tsaki wajen ganin Gwamna Ganduje ya yi nasara, 'yan siyasar biyu suka soma zaman 'yan-marina lamarin da, a karshe, ya kai su ga yin baram-baram.

Hasali ma, a zaben 2019 Sanata Kwankwaso ya tsayar da tsohon kwamishina a gwamnatinsa, Abba Kabir Yusuf takara a jam'iyyar PDP, ko da yake bai yi nasara ba.

A watan Janairu bayan wasu daga cikin manyan magoya bayan tsohon gwamnan sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, Gwamna Ganduje ya bugi ƙirjin cewa sun yi wa Sanata Kwankwaso ritaya a siyasance.

Ko da yake masu lura da lamuran siyasa na ganin akwai kuskure a game da kalaman Gwamnan ganin cewa Kwankwaso yana da miliyoyin magoya baya.

Asalin hoton, Dailypost

A ɓangare guda kuma, masu lura da harkokin siyasa na ganin tun da farko rikicin Mista Ambode da Sanata Bola Tinubu wani batu ne da kowa ya san inda za ta kaya ganin irin ƙarfin fada-a-ji da Tinubu yake da shi, ba kawai a jihar Lagos ba, har ma da yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya.

Ko da yake da farko Mista Ambode ya nemi ya ja da ubangidan nasa amma daga bisani ya mayar da wuƙa kubenta inda ya miƙa wuya lokacin da ta tabbata cewa Babajide Sanwo-Olu za a tsayar domin yi wa APC takara a 2019.

Da ma dai siyasar ubangida ba sabuwar aba ba ce a Najeriya, sai dai galibin lokuta ba a wanyewa lafiya idan muradun ubangidan da na yaronsa suka ci karo da juna, lamarin da kan yi mummunan tasiri kan yadda ake tafiyar da mulki da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga talaka.

Baya ga siyasar ubangida da yaron gida a matakin jiha, hakan yana faruwa ma a matakin gwamnatin tarayya inda su ma kusan duk kanwar ja ce.

Masu lura da lamura na ganin rikici irin na Mista Adams Oshiomhole da Gwamna Godwin Obaseki zai ƙare ne kawai idan suka ajiye buƙatu na ƙashin kansu sannan suka mayar da hankali kan yadda za su inganta rayuwar mazauna jihar, waɗanda da ma suke iƙirarin wakilta.