Coronavirus a Kano: Ganduje ya buɗe gidajen kallon ƙwallo

..

Asalin hoton, Abba Anwar

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin buɗe wuraren kallon ƙwallo da fina-finai a jihar duk da fargabar yaɗuwar cutar korona.

Wannan na zuwa a yayin da aka ci gaba da wasannin ƙwallon ƙafa a Turai inda mafi yawanci matasa ke kallo a gidajen da ake nuna wasannin a talabijin.

Sanarwar da Abba Anwar mai taimaka wa gwamnan kan harakokin watsa labarai ya fitar a ranar Asabar ta ce, gwamnan ya amince a buɗe wuraren kallon ne bayan wata ziyara da ƙungiyar masu gidajen kallon ƙwallon kafa suka kai masa a ofishinsa.

Sannan a cewar sanarwar, gwamnan ya bayar da takunkumi 40,000 a raba wa gidajen nuna kwallon ƙafa domin kiyaye shawarwarin da hukumomin lafiya suka bayar na rage yaɗuwar cutar.

A ranar 1 ga watan Yuni ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sassauta dokar kulle ta mako huɗu da ya saka a Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.

Ko a kwanakin baya sai da gwamantin ta Kano ta ce za ta fara bi gida-gida domin yi wa al'ummar jihar gwajin cutar korona.

A kwanakin baya an samu mace-macen jama'a ƙarai a Kano, sai dai Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya shaida wa manema labarai cewa kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen sun mutu ne sakamakon cutar korona, yayin da suke fama da wasu cutukan na daban.