Coronavirus a Kenya: ''Yan sanda sun fi cutar korona kashe mu'

Coronavirus a Kenya: ''Yan sanda sun fi cutar korona kashe mu'

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Al'ummar garin Mathare da ke Kenya sun fusata, kan yadda 'yan sanda ke cin zalinsu da kuma takura musu a lokacin kullen korona.

Babban abin da ya sa su fusata shi ne batun wani yaro mai shekara 13 da 'yan sandan suka harbe.

Jama'ar yankin sun koka da cewa korona ba ta shiga garin ba amma tuni ta yi sanadin mutuwar wani.