'Yan Syria: Muna fuskantar matsananciyar yunwa'

Syria

Asalin hoton, SUWAYDA24/AFP

Zanga-zanga ta sake barkewa a Syria saboda hauhawar farashin kayan abinci a daidai lokacin da darajar albashin ma'aikata kuma ke ƙara zubewa.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da jin ƙai ya yi gargadi cewa tasirin annobar Covid-19 ga tattalin arzikin duniya zai fi shafar kasashen da ke cikin rikice-rikice kamar Syria.

Gwamnatin Syria ta ce mutane kalilan ne suka kamu da cutar a ƙasar, amma an kiyasta cewa yaki ya yi barnar da ta zarce rabin dalar Amurka tiriliyan

Masu zanga-zanga a lardunan kudancin Syria na Deraa da Suwayda sun rika rera wakokin rashin amincewa da gwamnatin Bashar al Assad.

Kashi 90 cikin 100 na 'yan kasar na rayuwa cikin talauci ne, kuma yadda tattalin arzikin kasar ya ke daf da rugujewa gaba daya, da rashin abinci ne suka tilastawa jama'a sake fita bisa tituna.

Shugaban Hukumar bayar da agaji na MDD Sir Mark Lowcock ya ce ofishinsa ya nunka hasashen yawan mayunwata saboda dakatar da ayyukan kasuwanci saboda annobar Covid-19.

'Yan Syria na fuskantar matsananciyar yunwa fiye da duk wani lokaci tun da aka fara yakin basasar kasar. Farashin kayan abinci ya nunka kusan sau uku, sannan takardar kudin kasar ta fam ba ta da daraja.

Matsalar tattalin arzikin kasar Lebanon -- wadda makwabciyar Syria ce ya shafe ta matuka.

Ana kukan targade, sai ga karaya, domin a cikin makon nan Amurka ta sake kakaba wa gwamnatin Syria da kawayenta wasu sabbin jerin takunkumai wanda ka iya karasa tattalin arzikin -- matakin da ka iya sake daidaita sauran 'yan kasar da ke rayuwa cikin mawuyacin hali.