Yadda kasashen Turai ke kawo karshen kullen Covid-19

Sanya takunkumi ya zama abin da aka saba gani a kasashen Turai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanya takunkumi ya zama abin da aka saba gani a kasashen Turai

Kasashen Turai masu yawa za su bude iyakokinsu da makwabtansu na Tarayyar Turai a yau bayan shafe watanni da aka kullesu kuma aka hana tafiye-tafiye saboda rage yaduwar annobar Covid-19.

Hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai ta bukaci dukkan kasashen da ke cikin tarayyar da su kawo karshen matakan gaggawa da suka dauka, domin ta ce matakan ba su da tasirin da ake bukata saboda matakan bayar da tazara da kasashen suka fitar na cimma bukatun da ake da su na dakatar da bazuwar annobar.

A yau ne kasashen Croatia da Switzerlan da Jamus za su bude iyakokinsu baki daya - kuma jam'ian 'yan sanda da ma'aikata masu sa ido za su janye daga kan iyakokin nasu saboda sun kamala aikinsu.

Wadannan kasashen na cikin kasashen takwas na TT da matafiyi zai iya ziyarta daga Birtaniya ba tare da an killace shi ko an hana shi walwala ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An dawo da wasnnin kwallon kafa amma babu 'yan kallo

Sauran kasashen sun hada da Faransa, wadda ta bude iyakokinta da tsakar daren jiya, amma Faransar za ta killace matafiya daga Sfaniya da Birtaniya na mako biyu.

Kasashen Norway da Finland da kuma Denmark na kyale matafiya daga wasu zababbun kasashe ne a yau - amma ban da Sweden saboda sun ce akwai mutane masu yawa da suka mutu daga cutar Covid-19 a tsakanin al'ummar kasar.

Amma Portugal da Spain ba za su bude iaykkokinsu ba na tsawon mako biyu masu zuwa.

Sai dai Hukumar Gudanarwa ta TT ta so kasashen sun jinkirta bude iyakokinsu ga kasahen wajen Tarayyar daga wata mai zuwa.