An mutu sakamakon arangama tsakanin dakarun China da na India

Indian and Chinese soldiers

Asalin hoton, Getty Images

Sojojin India uku ne suka mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin dakarun kasar da na China a Ladakh da ke lardin Kashmir wanda ake takaddama a kansa.

Rundunar sojan India ta ce manyan jami'an sojin kasashen biyu suna "ganawa domin yayyafa ruwa kan wutar", tana mai cewa dukkan bangarorin sun yi asara sakamakon arangamar.

China bata bayyana cewa an samu asarar rayuka daga bangarenta ba, sai dai ta zargi India da tsallaka iyaka sannan ta kai hari kan sojojinta.

Kakakin ma'iakatar wajen kasar ya yi kira ga India da kada ta yi gaban kanta wajen daukar mataki ko kuma ta tayar da hargitsi.

An ambato mai magana da yawun na China, Zhao Lijian, yana cewa sau biyu India tana tsallaka iyaka ranar Litinin, "tana tsokanar fada da kuma kai wa jami'an China hari, lamarin da ya haddasa yin fito-na-fito tsakanin dakarun kasashen biyu da ke kan iyaka".

Lamarin na faruwa ne yayin da ake tsaka da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen biyu masu makaman nukiliya, wadanda a kwanakin baya suka yi cacar-baka a kan iyakokinsu ko da yake bata kai ga bude wuta ba.

India ta zargi China da aika dubban dakarunta yankin Ladakh inda ta ce China ta mamaye murabba'in kilomita 38,000 na yankinta.

Sau da dama ana ba-ta-kashi tsakanin bangarorin biyu a watan jiya.