#ArewaIsBleeding: An yi zanga-zanga a Katsina kan kashe-kashe

Zanga-zanga

Asalin hoton, Coalition of Northern Youth

Kungiyoyi da dama ne suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya ranar Talata da safe inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a turance, wato 'Jini yana kwarara a Arewa', sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai 'yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno.

Gwamnatin kasar ta sha cewa jami'an tsaro suna magance matsalar tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron 'yan bindiga ne, ko da yake 'yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Ranar Litinin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasara yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.

Wani rahoto da kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta fitar a watan jiya ya ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.

Asalin hoton, Coalition of Northern Youth

Asalin hoton, Coalition of Northern Youth