Tarayyar Turai ta fara binciken Apple kan 'bijirewa dokokinta'

Apple

Asalin hoton, Getty Images

Tarayyar Turai ta fara gudanar da bincike har kashi biyu kan zargin kamfanin fasaha na Apple da bijirewa wasu dokokinta.

An shiga da karar kan Apple da bijirewa wasu ka'idojin kasuwanci a Tarayyar Turai, da suka hada da salon yadda kamfanin ke sayar da kaya a shagonsa na intanet wato Apple Store.

Ana kuma zargin Apple da kin biyan kaso 300 da kamfanonin fasaha ke biya ga manhajojinsu, da kuma boye kayan da ke da araha ga masu shiga Apple Store din.

Masu shigar da koken sun kuma koka kan yadda kamfanin ya hana abokan hamayya amfani da manhajar biyan kudinta na Apple Pay.

To amma Apple ya nuna takaicin yadda Tarayyar Turai ta aminta da abin da ta kira koke marar tushe da abokan hamayya suka shigar.

Labarai masu alaka