Tarihin Hama Bachama da ake makokinsa a Adamawa

Hama Bachama Hakkin mallakar hoto Timawus Mathias
Image caption Ya zama Hama na Bachama a watan Disambar 2013

Al'ummar Bachama a jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya sun fara makokin kwana bakwai na Hama na Bachama - wato babban basaraken yankin, Mai Martaba Honest Irmiya Stephen.

Ana gudanar da zaman makokin ne kamar yadda yake a al'adar Bachama, idan Hama ya tafi gida, ma'ana ya mutu, kasancewar a al'adar Bachama ba a cewa Hama ya mutu.

Ita ma gwamnatin jihar Adamawa ta ayyana makokin kwana uku, domin jimamin mutuwar sarkin. Tuni dai aka fara makokin ranar Litinin din.

Masaraucin ya rasu ne ranar Lahadi bayan gajeriyar jinya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta'aziyya ga al'ummar masarautar ta Bachama bisa rashin sarkinsu.

Marigayin dai sarki ne mai daraja ta daya, kuma kasarsa ta hada da wasu yankunan kananan hukumomin Numan da Lamurde a jihar ta Adamawa.

Me al'adar Bachama ta tanada idan Hama ya mutu?

Hakkin mallakar hoto Timawus Mathias

A al'adar Bachama dai ba a cewa sarki ya mutu, sai dai a ce ya tafi gida, kamar yadda Timawus Mathias mai magana da yawun masarautar Bachama ya bayyana.

"To tafiyarsa gida an fara dawainiyar jana'izar sa, kuma shi ma shi ma hanyar al'ada ake bi, daga abin ya faru har a je a saukar da shi (binne shi), "a cewar Mathias.

Ana dai binne duk Hama na Bachama ne a ranar da ya tafi gida (ya mutu) wurin da ake binne Hama dake a garin Lamurde na jihar ta Adamawa. Kuma daga nan ake fara makokin Hama din na kwana bakwai.

Timawus Mathias ya ce masu zabar sarki ne suke yi hada sarki idan ya mutu. "Su ne suke daukar gawar su kai ta inda ake binne sarakuna."

Ya kara da cewa ana bukukuwan al'ada, amma ya musanta cewa babu miyagun al'adu da ake yi a lokacin makokin.

Timawus Mathias ya kara da cewa a al'adarmu a kwai gidajen sarauta shida.


"Saboda haka gidajen sarautar nan guda shida za ka ga suna wasa tsakaninsu, musamman matasa... suna kida suna rawa, sun fito da makamai kamar sharo irin na Fulani, wani ya dauki mashi, wani ya dauki adda, wani ya dauki sanda." a cewar Mathias.

Za su yi ta wasa tsakaninsu, suna wakoki, wasu suna yabon juna, wasu kuma suna yi wa juna dariya.

A lokacin da suke wannan wasan, su kuma masu zabar sarki na cikin suna kokarin hada sarkin.

Ana nade Hama na Bachama a cikin manyan riguna a matsayin likkafani. Kuma idan an kammala za a dauko gawar sarkin domin a sauke ta, ma'ana a binne ta, kamar yadda ake fada a al'adar Bachama.

Sai bayan kwana bakwai ne duk mai neman sarauta daga gidajen sarautar Bachama shida zai nuna aniyarsa bisa al'ada kamar yadda Mathias ya fada.

Wanene Hama na Bachama Honest Irmiya Stephen?

Hakkin mallakar hoto Timawus Mathias
Image caption Marigayi Hama na Bachama a lokacin yana dogarin gwamnan jihar Benue Kanar Abdullahi Shelleng
 • An haifi Hama na Bachma Honest Irmiya Stephen a shekarar 1954, kuma ya rasu yana da shekara 66.
 • Shi ne Hama na Bachama na 28.
 • Ya hau kan gadon sarauta a watan Disambar 2013.
 • Ya shiga aikin soja tun yana da kuriciya.
 • Ya yi yakin basasa na Najeriya
 • Ya halarci makarantar sojoji ta zaria, daga nan ya zarce zuwa makarantar horon sojoji ta Najeriya dake Kaduna NDA inda ya samu mukamin laftanar
 • Ya zama babban dogarin tsohon gwamnan jihar Benue Kanar Abdullahi Shelleng
 • Ya yi karatu a jami'ar Houston ta Amurka, inda ya karanci darasin kan zamantakewar dan adama.
 • Ya samu shaidar digiri biyu, da ta digiri na biyu ita ma guda biyu.
 • Alokacin rasuwarsa yana karatun digiri na uku.
 • Ya bar mata daya da 'ya'ya hudu, biyu maza biyu mata.

Gudunmawarsa ga masarautar Bachama

Babban abin da jama'ar masarautar Bachama suka karu da shi a lokacin Mai martaba Hama na Bachama Honest Irmiya Stephen shi ne zaman lafiya, a cewar Timawus Mathias.

Ya zama sarki a 2003 lokacin da al'ummar Bachama ke fama da tashe-tashen hankula.

A cewar Mathias sarkin ya yi kokari wajen hada kan al'ummar kasarsa. Ya ce Hama ya yi kokari wajn hada kan gidajen sarauta.

Ya kuma yi amfani da dukiyarsa wajen gyara gidan sarautar Bachama, sannan ya yi kokari wajen inganta alaka tsakanin masarautar Bachama da sauran masarautun arewacimn Najeriya, a cewar Mathias.

Ya kara da cewa jama'ar masarautar Bachama za su yi kewar Hama Honest Irmiya Stephen da wadannan halayen nasa.

Labarai masu alaka