China na 'tilasta wa Musulman Uighur tsarin iyali don rage yawansu'

An dauki wannan hoton ne tun a ranar 4 ga watan Yunin 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani tsohon hoto na wata mace tare da yaranta a China a arewa maso yammacin lardin Xinjiang

China na tursasa wa mata su yi amfani da ƙwayoyin hana haihuwa a yankin Xinjian a wani mataki na rage yawan musulman Uighurs, kamar yadda wani sabon bincike ya bankaɗo.

Rahoton wani malami a China Adrian Zenz ya janyo kiraye-kiraye daga sassan duniya cewa ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike na musamman kan abin da ke faruwa.

China dai ta musanta wannan zargin da rahoton ya yi, ta kuma ce "ba shi da tushe balle mkama".

Tuni ƙasar ke shan suka kan yadda ta tsare musulman Uighurs a wani sansani.

An yi amannar cewa akwai aƙalla mutum miliyan ɗaya 'yan kabilar Uighurs kuma mafi yawansu musulmai ne tsiraru, a wani abu da ƙasar ta kira sansanonin "ƙara ilimantarwa".

A baya, China ta musanta cewa akwai sansanonin ma, kafin daga baya ta kare su da cewa matakan dole ne na yaƙi da 'yan ta'adda, bayan rikicin 'yan a-ware a yankin Xinjiang.

Bayanan da ke cikin rahoton Mista Zenz ya haɗar da wanda aka samo daga jami'ai, da kuɗin tsare-tsare da kuma tattaunawar da aka yi da wasu mata 'yan kabilar Xinjiang.

Ya yi zargin cewa ana yi wa matan kabilar Uighur barazanar za a kai su gidan yari idan suka ƙi zubar da cikin da suke da shi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan Uighur na fuskantar mummunan tsarin takaita haihuwa kamar yadda marubucin ya bayyana

Ana cewa matan da ke da yara ƙasa da biyu ana barinsu a hukumance su sha maganin zubar da ciki bisa raɗin kansu, su kuma sauran ana tilasta musu shan maganin ko kuma yin tiyatar hana ɗaukar ciki.

Daga bayanan da Mista Zenz ya tattara, tun gabanin wannan lamari adadin mutanen da ke yankin Xinjiang ya ragu sannu a hankali cikin shekarun baya.

Inda adadin ya ragu da kusan kashi 84 cikin 100 a manyan yankuna biyu na Uighur tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 kuma ya ci gaba da raguwa a 2019.

A tsohon sansanin da ake tsare mutanen da ke yankin Xinjiang, an ce allura ake yi wa matan don a tsayar da jinin al'adarsu, saboda yawan zubar jini akai-akai na da tasiri ga aikin ƙwayoyin da ke hana haihuwa.

"Duka dai, hukumomi a Xinjiang na yin wannan azabtarwar ne da sunan kare mata daga haihuwar yara sama da uku," in ji rahoton.

'Yan siyasa na ta kiran MDD ta yi bincike

A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, wasu jam'iyyun siyasa da kungiyoyin duniya da wasu 'yan siyasa ciki har da wakilin Amurka Sanata Marco Rubin, sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike ba tare da nuna son rai ba cikin wannan al'amarin".

China na fuskantar matsin lamba kan yadda take muzgunawa 'yan kabilar Uighurs a baya-bayan nan.

A wani bincike da BBC ta gudanar cikin 2019, ta gano cewa ana raba yara da iyayensu cikin dabara a wani mataki na fitar da su daga al'ummarsu ta musulmai.

Wani ɓoyayyyen sansanin da ake tsare mutane

A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AP ya wallafa ranar Litinin, Ana cin tarar matan kabilar Xinjiang ko kuma yi musu barazanar ɗauri, idan suka karya dokar taƙaita mallakar 'ya'ya.

Gulnar Omirzakh, haifaffiyar ƙasar China ce, an kuma umarce ta da shan kwayoyin hana haihuwa bayan ta haifi yaronta na uku kamar yadda rahoton AP ya bayyana.

Shekara biyu bayan nan a watan Janairun 2018, wasu jami'an soji suka ƙwanƙwasa mata gida tare da ba ta takardar cin tararta kudi da suka kai fam 2,000 saboda haihuwar yara sama da biyu.

An kama mijinta a baya, inda aka tsare shi. Ita kuma Gulnar sai aka yi mata barazanar daure ta a inda ake tsare da mai gidanta idan ba ta biya kudin ba.

Labarai masu alaka