Za ku dinga jin labaran BBC kyauta a manhajar MyMtn

Labarai cikin minti Ɗaya Hakkin mallakar hoto BBC/MTN
Image caption Masu sauraro za su samu damar sauraron labaran BBC cikin minti ɗaya akai-akai daga safe zuwa dare ta manhajar MyMTNApp

Sashen BBC da ke watsa labarai ga ƙasashen duniya ya ƙulla ƙawance da kamfanin sadarwa na MTN da ke Najeriya don jin labaran BBC cikin minti ɗaya a kyauta cikin Turanci da Hausa da Igbo da Pidgin da kuma Yorabanci ga waɗanda suka sauke manhajar MyMTNApp a wayoyinsu.

Wannan ne karo na farko da wata babbar kafar watsa labarai ta duniya za ta kasance cikin manhajar ta MyMTNApp.

Labaran BBC a minti ɗaya yana sanar da dumbin masu sauraron kafar irin abubuwan da suke faruwa kuma ake tattauna su a kafafen sada zumunta na zamani har ma da irin labaran da suke faruwa a Najeriya da ma sauran ƙasashen duniya.

Za a riƙa sabuntawa kowace rana tsawon mako ɗaya. Wannan tsari zai sanar da ɗumbin masu sauraron BBC a Najeriya sabbin labaran wasanni da nishadi da kimiyya da batutuwa da dama.

Masu sauraro za su samu damar sauraron labarai cikin minti ɗaya akai-akai daga safe zuwa dare.

Masu jin Hausa da Igbo da Pidgin da Yarabanci ne za su ci gajiyar wannan yarjejeniyar ta hanyar samun ƙayatattun labarai cikin daƙiƙa 60 a sauƙaƙe ba tare da wata matsala ba.

Hadin gwiwar za ta tabbatar cewa masu amfani da layin MTN za su samu sahihan labarai daga BBC musamman yadda ake samun ƙaruwar labaran ƙarya a sassan Najeriya da Afirka.

MTN Nigeria shi ne babban kamfanin sadarwa a nahiyar Afirka wanda ke sada sama da mutum miliyan 64 daga sassa daban-daban na Najeriya da junansu da ma duniya.

Ya samar da manhajar MyMTNApp wadda sama da mutum miliyan hudu ke amfani da ita.

Oluwatoyosi Ogunseye, Shugabar BBC reshen Afirka ta Yamma ta ce "wannan yarjejeniya da MTN tana daga cikin burin BBC na kusanto da masu sauraro a duk inda suke. Ɗaya ne daga cikin hanyoyin da BBC ke ba da gudummawa a Najeriya kuma muna matuƙar farin ciki da wannan hadin gwiwa saboda dama ce ta ƙara janyo masu saurarenmu a Najeriya musamman matasa garemu."

Da yake jawabi kan yarjejeniyar, babban jami'in da ke kula da hanyoyin sadarwa na kamfanin MTN, Srinivas Rao ya bayyana cewa "muna alfahari da wannan ƙawance . Wata hanya ce da zamu bai wa matasan Najeriya damar sauraron labarai masu sahihanci. A zamanin da ake yawaita yaɗa labarai marasa tushe musamman a shafukan sada zumunta, irin wannan tsari zai kawo sauye-sauye da dama."

Labarai masu alaka