Illar muhalli: Yadda gubar dalma ke kashe yara 'yan Afirka

  • Daga Navin Singh Khadka
  • Wakili kan Muhalli, BBC World Service
Yadda ake amfani da tsoffin baturan mota a jihar Bihar ta India

Asalin hoton, Pure Earth

Bayanan hoto,

Ta'ammali da tsoffin baturan mota na daga cikin abin da ke janyo gubar dalma

Bincike ya gano cewa a cikin yara a kan samu yaro guda da gubar dalma ta yiwa illa.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Pure Earth, sun kiyasta cewa wannan bala'i na gbar dalma zai iya shafar yara miliyan 800 musamman a kasashen da ke tasowa.

Kasashen gabashin Asiya sune abin zai fi shafa inji su.

Rahotanni sun ce ta'ammali da matattun baturan mota ko abubuwan da aka hako marassa amfani na daga cikin abin da ke janyo gubar dalma.

Tsoffin baturan mota sune kashin bayan gubar dalma

Wasu masu bincike sun fitar da rahoto bayan da aka gwada jinin dubban yara da aka zabo a sassan duniya.

An fitar da rahoto ne a kan irin illar da ke tattare da gubar dalma.

Bincike ya gano cewa kananan yara 'yan kasa shekara biyar su suka fi hadarin kamuwa da cutar gubar dalma.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Baya ga kasashen da ke gabashin Asiya wanda su ne a gaba wajen samun masu dake da gubar dalma a tare da su, sai Afirka.

Binciken da aka yi da ya gano cewa cutar gubar dalma zata shafi yara miliyan 800 a sassan duniya, kaso daya bisa ukunsu a Afirka suke.

A cikin kasashe 14 da ake samun wannan cuta, shida daga cikinsu kasashen Afirka ne a cewar rahoton hadin gwiwa na Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef.

Najeriya ce a sahun gaba a kasashen Afirkan da ke da wannan cuta inda miliyoyin yara kan kamu da ita.

Gubar dai ta fi yiwa yara 'yan kasa da shekara biyar illa ind ata ke lalata musu kwakwalwa.

Binciken ya ce yadda ake amfani da tsoffin batiran mota da kuma wasu abubuwa da suka shafi lantarki shi ke janyo a samu guba dalma.

Wasu masu bincike sun shaida wa BBC cewa, mafi yawancin yaran Afirka na aiki ne a garejin mota ko kuma wani waje da ake ta'ammali da wasu karafa da suka tsufa.

Wani jami'i a Ghana da ke aiki a ma'aikatar kula da muhalli ta kasar ya ce fiye da kaso 60 cikin 100 na wadanda ake samu da gubar dalma sun samu ne saboda amfani da ake da cokulan wuraren cin abinci saboda ana yin irin wadannan cokulan ne da sanhoron da aka gama amfani da shi.

Kazalika wani jami'i ma a Senegal ya ce fentin da ke da sinadarin dalma a cikinsa, na daga cikin abubuwa masu guba da ke haddasa gubar dalma kuma tana yi wa yaran Afirka illa.

Ya ce zaka ga idan an yi fenti mai dauke da sinadarin dalma yara kan taba sannan su sanya a bakinsu abin da ke musu illa.

Asalin hoton, Pure Earth

Bayanan hoto,

Gubar dalma na kasancewa a kasa ko ruwa

Binciken ya ce akwai bukatar daukar matakin gaggawa wajen kawo karshen wannan illa da gubar dalma kan yiwa yara.

Rahoton ya ce yaran da ke zaune a wuraren ko kuma kusa da wajen da ake ta'ammali da abubun da ke dauke da gubar dalma za aka idan har za a yi musu gwaji to za aga alamar gubar.