Champions League: Barcelona za ta kara da Bayern Munich

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hakan ya faru ne biyo bayan ragargazar da Bayern ta yi wa Chelsea da ci 7-1 a wasa gida da waje

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich za ta barje gumi da Barcelona a wasan dab da na kusa da na karshe ko kuma kwata fayinal na gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.

Hakan ya faru ne biyo bayan ragargazar da Bayern ta yi wa Chelsea da ci 7-1 a wasa gida da waje.

Bayern ta cinye Chelsea 3-0 a wasan farko da aka buga a Stamford Bridge sannan ta sake yin wujuwuju da ita a filin wasa na Allianz Arena a daren jiya Asabar da ci 4-1.

Barcelona ta samu kaiwa kwata fayinal ɗin ne bayan ta doke Napoli.

Barcelona da Beyern za su buga wasansu a babban birnin Portugal wato Lisbon a mako mai zuwa kuma wasa ɗaya za a yi - ba gida da waje ba kamar yadda aka saba - ku ma kun san korona ce ta jawo.