Juventus ta naɗa Andrea Pirlo a matsayin kocinta

Andrea Pirlo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An naɗa Pirlo ne bayan korar Maurizio Sarri ranar Asabar

Juventus ta naɗa Andrea Pirlo a matsayin kocinta bayan ta sallami Maurizio Sarri.

Mako guda kenan da naɗa Pirlo a matsayin kocin ƙungiyar ta 'yan ƙasa da shekara 23.

Zakarun Italiya sun kori Sarri ne bayan ya yi kaka ɗaya kacal a ƙungiyar duk da cewa ya lashe Serie A, sai dai an fitar da ita daga Champions League ranar Juma'a tun a zagayen 'yan 16.

Pirlo mai shekara 41 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu har zuwa 2022.

Juventus ta ce hukuncin ɗaukaka tsohon tauraron ɗan wasan Italiya da AC Milan ɗin ya zo ne sakamakon "Pirlo yana da ƙwarewar da zai iya jan ragama tun daga sanda ya fara mnurza leda".