Buruji Kashamu: Takardar ta'aziyyar da Obasanjo ya rubuta na jawo ce-ce-ku-ce

Olusegun Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Da alama takardar da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubuta dangane da rasuwar Sanata Buruji Kashamu ta ɓata wa mutane da dama rai, wasu kuma na goyon bayan tsohon shugaban.

A wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar Kehinde Akinyemi ya fitar, ya bayyana cewa duk da cewa mutuwa babu daɗi, amma rayuwar Kashamu da tarihin da ya bari ya zama darasi ga mutane.

Kashamu ya rasu ne sakamakon cutar korona a ranar Asabar, 8 ga watan Agustan 2020, a asibitin First Cardiology Consultants da ke Legas, kamar yadda abokinsa Sanata Ben Murray Bruce ya tabbatar.

A cewar Obasanjo, "lokacin da Kashamu ke da rai, ya yi amfani da doka da siyasa domin guje wa zargin da ake yi masa na laifuka da ya aikata a Najeriya da kuma ƙasashen ƙetare.

"Amma babu wata doka ko siyasa da al'ada ko wani al'amari na yau da kullum ko kuma rashin lafiya da ta hana mutuwa ɗaukar ransa a daidai lokacin da ubangiji ya ce lokacinsa ya yi."

"Allah ya gafarta masa zunubansa kuma ya sa shi Aljannah, kuma ya ba iyalansa haƙurin wannan rashi," in ji Obasanjo.

Asalin hoton, olusegun obasanjo

Sai dai ko da BBC ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun Obasanjo wato Adeyemi kan wannan lamari, ya ce "Obasanjo na da ra'ayinsa kan ko wane irin mutum, (ko rayayye ko matacce)".

Ya kuma ce masu caccakar Obasanjo a kafafen sada zumunta su ma suna da bakinsu kuma Obasanjo ba ya da na sani kan wannan takarda da ya rubuta.

Kafin mutuwar Sanata Kashamu, ya kasance ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Ogun ta gabas.

Ya kuma kasance ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar PDP a 2019 a jihar Ogun.

Yadda mutane ke mayar wa Obasanjo martani

Tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose ya yi wa tsohon sanatan addu'a, sai dai ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da sanarwar da Obasanjo ya fitar.

Da dama daga cikin mutane a shafukan sada zumunta sun yi hannun riga da kalaman na Obasanjo.

@OgbeniDipo cewa ya yi ko maƙiyin Obasanjo ya mutu, ba zai yafe masa ba.

Wannan kuma shaguɓe ya yi inda ya ce da a ce waɗannan kalaman daga wurin ubangiji suke, da babu damuwa, amma abin damuwar shi ne ɗan adam wanda zai iya mutuwa shi ne yake faɗan haka. Kada ka damu Baba, baza ka mutu ba har abada.

Sai dai kuma akwai wasu da suke da ra'ayi irin na Obasanjo

Wannan cewa ya yi abin da Chief Olusegun Obasanjo ya ce kan Buruji Kashamu gaskiya ne kuma duk ɗaya ne ga duk wani ɗan Najeriya mai cin rashawa.

Akasarinsu suna amfani da doka da siyasa wurin kauce wa shari'a da kuma zarge-zargen laifukan da ake yi musu, amma ba za su iya guje wa mutuwa ba.