'Akwai ayar tambaya kan kudaden tallafin korona a Najeriya'

Kudin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

A Najeriya, ƙungiyoyin da ke bin diddigi kan yadda hukumomin ƙasar ke kashe kuɗaɗen yaƙi da annobar korona na dasa ayar tambaya game da gaskiyar al'amarin.

Duk da yake tun bayan ɓullar cutar korona Najeriya a ƙarshen watan Fabrairu, kawo yanzu babu ƙayyadajjen adadi na yawan kuɗin da gwamnati da ɓangarorin 'yan kasuwa masu zaman kansu suka zuba a shirin yaƙar annobar, mutane da dama na cewa an zuba biliyoyin kudi.

Kwamared Kabiru Saidu Dakata, na ƙungiyar CAJA, ya shaida wa BBC cewa, akwai almundahana a yadda ake tafiyar da harkar korona a Najeriya.

Ya ce "Rashin yin abubuwa a buɗe da shugabanni a matakai daban-daban suke fakewa a kai inda suke cewa ana rabawa mutane tallafi bayan jama'a basu gani a kasa ba, shi yasa ma mutane ke cewa basu yarda da koronar ba ma".

Kwamared Kabiru, ya ce mutane na jin an ce an bayar da kuɗi tallafin korona, amma ba su gani a ƙasa ba, shi yasa suke gani cewa gwamnati ce kawai ke amfana alhali su an kulle su a gida an hana su fita domin su je su nemi na kansu.

Kabiru Sa'idu Dakata ya ce " Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane suka ƙi gasgata batun korona, suna gani kawai idan ma akwai ta to sai dai a wasu ƙasashen domin su suna gani shugabannisu na amfani da batun koronar ne suna samun kudi".

Ya ce, saboda irin wannan almundahana da ake yi a bangaren gwamnati, shi yasa suke hada hannu da kungiyoyi ko hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa domin bankado irin haka.

Tuni dama dai mutane ke ta korafi a kan batun kudaden tallafin da aka bayar domin yaki da cutar korona, inda mutane ke cewa su basu gani a kasa ba.

Kuma duk wani tallafi na abinci ko kudi da gwamnatin tarayya ko gwamnatocin jihohi suka ce suna bai wa mutane, mutane sun ce sam basu san ana yi ba.

Abin tambayar anan shi ne shin ina kuɗaɗen da aka samu daga mashahuran mutane a kasar da kuma kungiyoyi masu zaman kansu?