Shugaban Faransa ya yi tur da kashe ma'aikatan agaji 8 a Nijar

Car

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto,

An ga wannan motar da aka kona a kusa da wurin da aka kai harin

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi tur da harin da aka kai wa ma'aikatan jin ƙai a Nijar, inda ya bayyana lamarin a matsayin na matsorata.

Ya kuma ce zai yi duk abin da zai iya yi don yin ƙarin haske kan wannan hari da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas, shida Faransawa da kuma biyu 'yan Nijar.

Shugaban na Faransa wanda ya zanta da takwaransa Mahamadou Issoufou na Nijar ya ƙara da cewa ya duƙufa wajen taimakawa don murƙushe "ƙungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel".

Hukumomi sun ce wasu mahara ne a kan babura suka far wa mutanen takwas ciki har da ma'aikatan ƙungiiyar agaji a wani yankin da ke da ragowar raƙuman dawa cikin Afirka ta Yamma.

Sun dai ce sun tura ɗumbin jami'an tsaro don bin sawun maharan da suka bi duhun daji suka tsere bayan hallaka mutanen da ƙone motarsu.

Ƙungiyar agajin Faransa ta ACTED ta ce akwai ma'aikatanta da dama cikin waɗanda aka kashe yayin wata fita don yawon buɗe idanu.

An yi imani shi ne hari irinsa na farko da aka kai wa Turawa 'yan ƙasashen Yamma a yankin, wanda fitaccen wuri ne a tsohuwar ƙasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

Gwamnan Tillaberi, Tidjani Ibrahim Kachalla ya ce suna tunkarar lamarin, kuma za su fitar da ƙarin haske game da wannan hari, wanda bai ce ga ƙungiyar da ta kai shi ba.

Wata majiya a kusa da hukumomin kula da muhalli ta Nijar ta ce harin ya faru ne da misalin 11:30 a wani wuri mai nisan kilomita shida gabas da garin Koure, wanda ba shi da nisa daga Niamey.

Majiyar ta fada wa AFP cewa an harbe akasarin mutanen da harin ya ritsa da su ne.... Tana cewa sun ga jigidar harsasan da ta ƙare an yasar da ita a wurin.

A birnin, wani mai magana da yawun dakarun sojin Faransa ya ce rundunar tsaro ta Barkhane da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, na ba da goyon baya ga dakarun sojan Nijar.

AFP ya rawaito mutanen yankin na tabbatar masa cewa sun ga jiragen yaƙin Faransa na shawagi ta sama da yammacin ranar Lahadi yayin da sojojin Nijar suke bincika daji.