Fashewar sinadarai a Beirut: Ana cigaba da zanga-zanga, yayinda ministoci ke murabus

Rikici ya sake mamaye titunan Beirut a rana ta biyu a jere

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Rikici ya sake mamaye titunan Beirut a rana ta biyu a jere

Sama da mutum 200 aka tabbatar sun mutu sakamakon fashewar da aka samu a Beirut na kasar Lebanon, a cewar gwamnan birnin.

Marwan Abboud ya ce har yanzu ana laluben mutanen da suka bata, akasari baki daga kasashen ketare.

Murabus din ministoci uku kawo yanzu da na 'yan majalisa bai sauya komai ba.

Akwai rahotannin da ke cewa ministan kudi Ghazi Wazni na shirin mika takardar ajiye aiki, gabanin taron majalisar ministoci da firaminista Hassan Diab zai jagoranta kan rikicin kasar.

Masu bayar da tallafi a duniya sun alkawarta ba da tallafin euro miliyan 250 ga Lebanon, kwana biyar da aukuwar fashewar da ta ɗaiɗaita wani gagarumin yanki a Beirut.

Sai dai a wani taron tallafi da Faransa ta jagoranta ta intanet ta bukaci a samar da sauye-sauye.

Fashewar ta auku a inda aka ajiye ton fiye da 2,000 na wasu sinadiran Ammonium Nitrate na tsawon shekaru shida kuma su suka janyo wannan barna.

An shiga rana ta biyu na rikici a Beirut.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Matasan da ke gangamin tilasta wa gwamnati ta yi murabus na jifan 'yan sanda da fasa shaguna a tsakiyar Beirut, sannan masu zanga-zanga sun yi kokari kutsa wa a inda aka sanya shingen haramta shiga ginin majalisa. An samu tashin gobara a wajen tarzomar.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga, yanayin dai kusan maimaicin abin da aka gani ne a boren ranar Asabar.

Shugabanin kasashe 15 a taron tallafin, da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya jagoranta, sun alkawarta ''ba da tallafi mai kauri'' a cewar sanarwar.

''Taimakon ya kasance kan lokaci, isassu, sannan akai-akai bisa bukatun al'ummar Lebanon,'' a cewarsa, ya kuma kara da cewa taimakon ''zai je kai tsaye ne ga 'yan Lebanon, a gaggauce ba tare da wani boye-boye ba''.

Sanarwar ta kuma kara da cewa masu bada agajin a shirye suke su taimakawa Lebanon a tsawon lokacin farfadowarta in dai gwamnati ta saurari bukatun sauye-sauye da 'yan kasar ke hankoro.

Ofishin Shugaba Macron ya ce Faransa ta karbi kudaden da yawansu ya kai €252.7m ($297m, £227m) a wajen taron.

Jami'ai sun kiyasta cewa fashewar ta haifar da asarar dala biliyan 15.

Mutane 158 suka mutu, 6,000 sun mutu sannan an rasa gidaje 300,000. Bayanai sun tabbatar da cewa an ajiye sinadarin ammonium nitrate a dakin ajiya na tsawon shekara shida duk da gargadi da aka yi cewa yana da haɗari.

Bayanan bidiyo,

Masu aski sun nuna yanayi da suke ciki lokacin da aka samu fashewar

Lebanon na cikin yanayi na matsalar tattalin arziki irin sa mafi muni tun yaki basasar kasar tsakanin 1975-1990, akwai matsalar wutan lantarki, babu ruwan sha mai tsafta ga kuma lalacewar asibitoci.

Darajar kudin kasar ya karye, kuma kasar ta kasa biyan basukan da ake bin ta wadanda wa'adinsu ya cika tun a watan Maris. Tattaunawa da asusun lamuni na IMF kan karbar bashin dala biliyan 10 ya tsaya cak.

Akwai fargabar cewa iftila'in fashewar da aka samu a kasar ya sake kassara kokarin farfado da tattalin arzikinta.

Gwamnati ta soma rasa ministocinta a cikin tsananin yanayin da take ciki.

Ministan Muhalli, Damianos Kattar shi ne mutum na biyu da ke murabus daga gwamnati a ranar Lahadi.

Barinsa aiki na zuwa ne bayan ministan yada labarai Manal Abdel Samad wadda ta fito da gazawar sauye-sauyen gwamnati ta ce ba za ta iya ci gaba da rike mukamin ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Manal Abdel Samad ita ce minista ta farko da ta yi murabus

Su waye suka yi alkawari?

Wasu daga cikin alkawuran da aka dauka a wajen taron sun hada da:

 • Tarayyar Turai - karin tallafin €30m ($35m, £27m), a kan €33m da ta alkawarta da fari
 • Burtaniya - karin £20m; £5m kudin tallafin da ta sanar da fari a wancan makon
 • Jamus - €10m; €1.5m da farko
 • Faransa - za ta bada kayan gine-gine, magunguna da tallafin abinci
 • Spaniya - za ta aike da alkama da kayan gida da magunguna
 • Switzerland - $4.38m
 • Amurka - $15m
 • Qatar - $50m
 • Kuwait - $40m
 • Denmark - €20m
 • Norway - €6.5m

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da dala miliyan 100 ake bukata domin ayyukan gaggawa, kamar samar da abinci da ruwan sha, da kuma gine-gine da samar da asibitoci da makarantu.

An gudanar da taron ne ta intanet saboda annobar korona.

Shugaba Macron, lokacin da yake magana daga gidansa da yake hutun bazara a kudancin Faransa, ya bukaci a kaddamar da bincike mai zaman kansa da sahihanci kan yadda aka samu aukuwar fashewar.

Faransa ce ta raini kasar, kuma Mista Macron shi ne shugaban kasa na farko da ya ziyarci Beirut bayan iftila'in.

Sai dai shugaban Lebanon Michel Aoun ya yi watsi da batun bincike daga ketare.

A tsokacinsa kan zanga-zangar ranar Asabar, shugaban Faransa ya ce zabi ya rage ga gwamnati ''na amsa bukatar 'yan kasa na neman 'yancinsu, da kuma boren da suke a Beirut.''

Sai dai ya kara da cewa tayar da zaune tsaye ko tarzoma ba za su kawo wanzuwar zaman lafiya a kasar ba, ya kara da cewa: ''Makomar Lebanon na cikin hadari.''

Shugaba Trump shi ma ya shiga taron tare da yin kiran kaddamar da sahihin bincike, shugaban ya ce Amurka za ta taimaka, a cewar sanarwar Fadar White House.

''Shugaban ya bukaci a kwantar da hankula a Lebanon da kuma nuna aminta da zanga-zangar lumana bisa dokoki, a cewar sanarwar.