Kalaman Diezani kan 'yan yahoo-yahoo sun jawo ''mata tsana'' a Najeriya

Diezani Alison-Madueke

Asalin hoton, SAMUEL KUBANI

Bayanan hoto,

Tun 2015 aka gurfanar da Diezani Alison-Madueke a kotu kan zargin almundahana a lokacin da take ministar man fetur

'Yan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta na ta ce-ce-ku-ce kan tsohuwar ministar man fetur ta ƙasar Diezani Alison-Madueke.

Hakan ya biyo bayan wani bidiyo ne da ya ɓulla tana Allah-wadai da 'yan zambar intanet waɗanda ake kira yahoo-yahoo, inda ta ce 'yan Najeriya suna dogara da su.

Wasu na sukarta cewa ita ma kanta tana fuskantar shari'a gamne da cin hanci da rashawa amma kuma take da bakin magana.

Wani mai suna Dr. Dípò Awójídé (@OgbeniDipo) ya ce: "Wadda ke gudun shari'a ce ta samu bakin magana saboda babu wasu tsauraran hukunci kjan satar kuɗin Najeriya.

Adejumo Abayomi (@AdejumoAbayomi4) ya ce: "Matar da ya kamata a ce tana gidan yari ita ce take cewa wai 'yan Yahoo sun zama abin koyi a Najeriya. Ba laifinta ba ne."

Me Diezani ta ce?

Yayin wani taro da ƙungiyar cigaban ƙabilar mai suna Ijaw National Development Group ta shirya ta intanet, tsohuwar ministar ta ce dalilin da ya sa 'yan Najeriya ba sa tsinana wa ƙasar komai saboda matasa sun koma koyi da 'yan Yahoo.

Ta ce 'yan zambar intanet ɗin Yahoo na ƙara yawan laifuka a ƙasar kuma hakan ba alkairi ba ne ga Najeriya.

Mawallafin jaridar Point Black News ne mai suna Jackson Ude ya fara wallafa bidiyon a Twitter.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda shi ne ya ba ta minista, shi ma ya halarci taron ta intanet.

'Ku karɓi saƙon ku ƙyale ɗan aiken'

Asalin hoton, AFP

Wasu daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari ma sun tofa albarkacin bakinsu, inda Bashir Ahmad ya ce ya kamata mutane su yi aiki da saƙon su ƙyale ɗan aiken.

Bashir Ahmad mai taimaka wa Buhari ne kan kafafen sada zumunta.

Shi ma mai bai wa Buhari shawara kan kafafen sada zumunta, Tolu Ogunlesi ya ce Dizeani ta zama mai kalaman ƙarfafa gwiwa ta 'yan Yahoo.

Zargen-zargen cin hanci a kan Dizeani

Madam Diezani ta koma Birtaniya da zama tun a shekarar 2015 kuma ana zarginta da almundahana yayin da hukumar EFCC ta zarge ta wasu laifukan daban.

Lamarin ya samo asali e tun a 2014 lokacin da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN, Sanusi Lamido Sanusi ya yi zargin cewa dala biliyan 20 ta kuɗin man fetur sun ɓata a ƙarƙashin Dizeani - lokacin tana ministar man fetur.

Tun daga lokacin en kuma EFCC ta nemi kotu ta sahale mata don ta ƙwace kadarorinta ciki har da sarƙoƙi da suka kai dala miliyan 40.

Kazalika tana fuskantar shari'ar almundahana ta hanyar mallakar kadadarori ba ta hanyar da ta dace ba a wata kotun Birtaniya.