Direbobin dakon mai sun janye yajin aiki a Legas

PMS

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Najeriya dai na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziƙin man fetur a duniya

Direbobin da ke dakon man mai daga jihar Legas sun janye yajin aikin da suka shiga bayan tattaunawa da gwamnatin jihar.

Ƙungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG ta janye yajin aikin ne da yammaci Litinin ranar da ta ce za ta tsunduma cikin yajin aiki saboda matsalolin rashin kyawon hanya, bata-gari da takurar jami'an tsaro a kan hanya.

Wakilin BBC a Legas ya ce ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawar da shugabannin ƙungiyar suka yi da ɓangaren gwamnati.

Gwamnati kuma ta yi alƙawarin diba buƙatunsu tare da magance su.

A ranar Juma'ar da ta gabata kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG, ta ce za ta dakatar da ayyukanta a Legas da sauran yankuna saboda matsalolin rashin kyan hanya, bata gari da takurar jami'an tsaro a kan hanya.

Kungiyar ta ce wannan yanayi ya haifar da kunci da jefa damuwa tsakanin direbobin da ke dakon mai zuwa jihohi tsawon watannin yanzu, duk da korafin da suka sha gabatarwa mahukunta.

Shugaban masu gidajen mai na kasa, Bashir Dan Mallam, ya shaida wa BBC cewa idan direba ya yi lodi sai ya kashe sama da dubu 100 wajen sallamar jami'an tsaro wanda hakan kuma gaskiya na shafar ayyukansu.

''An sha kai korafi wajen hukumomi amma babu abin da ya sauya ko da yake har yanzu tattaunawar ba ta daina ba muna kai.''

Mallam Bashir ya ce, idan aka daina dakon man to wannan zai shafi arewa da ko ina a Najeriya tun da wuraren da ake lodin a kasar, bakin ruwa ne sannan a rarraba man a yankunan kasar.

Tasirin yajin-aikin

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ba shi ne karo na farko da kungiyoyin kwadagon ma'aikatan man fetur ke shiga yajin aiki ba a Najeriya, kuma a duk lokacin da suka shiga to ana fuskantar matukar wahalar man a kasar.

Akwai dai al'ummomi da dama da ke amfana daga wannan harka don haka idan aka ce yau ana dakatar da komai to akwai matsala, in ji Mal. Bashir.

Sannan ya ce a arewacin Najeriya za a samu matsala sosai, duk da cewa kamfanin mai na kasa wato NNPC ya bukaci a bude rumbunansa da ke ko'ina a fadin kasar.

''Idan aka ci gaba da hakan dole za a rinka samun nakasu ko da yake ba ma son abin ya yi nisa.''

''Jami'an tsaron da ke takura wa direbobi, sai kaga direba da ya dauko mai ya yi asarar sama da dubu 100 to idan wannan ya cigaba da sauran zarge-zarge dole a rinka samun koma baya.''

Tattaunawa

Bayanai sun nuna cewa hukumar man fetur ta kasa wato NNPC ba ta son yajin aikin ya yi nisa saboda matsalolin da hakan ka iya sake haifarwa a kasar.

Rahotannin dai sun tabbatar da cewa ana tattaunawa tsakanin hukumar da bangarorin masu korafi ko neman ganin an biya musu bukatunsu.

Yajin aikin direbobin zai shafi kusan dukkanin jihohin kasar saboda galibin man da ake shigarwa jihohi daga Leags ake dakonsu

Najeriya dai na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziƙin man fetur a duniya, sai dai matatunta sun rufe ko kuma ba sa aiki yadda ya kamata, abin da ya sa ƙasar ta yi matuƙar raja'a a kan man da ake sarrafa a ƙetare sannan a sake siyar mata

Karin bayani

An dai jima ba a shiga wahalar man fetur a Najeriya ba ko a iske ababen hawa na rige-rigen shan mai saboda fargabar karancinsa.

A duk lokacin da aka fuskanci irin wannan barazana, hukumomi na kokarin ganin yadda za su shawo kan matsalar saboda gudun shiga cikin wahalar man.

Kuma a wannan lokaci ma da alama ba lallai yajin aikin direbobi ya dau lokaci ko ya yi tasiri ba lura da tattaunawar shawo kan matsalar da suke yi da hukumomi.

Karin labaran da zaku so karantawa