Ridda a Kano: An yanke wa mawaƙi hukuncin kisa bisa yin ɓatanci ga Annabi

Zanga-zanga a Kano

Asalin hoton, IDRIS IBRAHIM

Wata babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W. tare da wani da ya yi ɓatanci ga Allah.

Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar wa BBC da hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar ɗaukaka ƙara.

"An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka," in ji Jibo Ibrahim.

"A halin yanzu za a rataye shi har sai ya mutu, kamar yadda sashe na 382 (b) na kundin shari'ar Jihar Kano ta shekara ta 2000 ta tanada.

Tun a watan Maris na 2020 ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge shi da yin ɓatancin a cikinta.

Kazalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Alƙali ya yanke wa Umar Farouq hukuncin ne sakamakon shekarunsa ba su kai 18 kamar yadda kundin manyan laifuka ya tanada.

Ya yi ɓatancin ne yayin da suke yin ce-ku-ce da wani.

Zanga-zangar Allah-wadai

Asalin hoton, Idris Ibrahim

Bayanan hoto,

Hukumar Hisbah ta bukaci mazauna jihar kada su yi gaban kansu wajen yanke hukunci

Tun a watan Maris ne matasa suka yi sun yi zanga-zangar neman a hukunta wani Yahaya Sharif-Aminu, wanda suka zarga da yi wa Annabi Muhammad S.A.W batanci.

Matasan sun yi cincirundo ne a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda kwamandan hukumar ya tarbe su.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa suka far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano tare da lalata abin da ke ciki.

'Hukuncin zai zama izina ga sauran jama'a'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dukkanin mutum biyu da aka yanke wa hukuncin na da damar ɗaukaka ƙara

Shugaban mutanen da suka yi zanga-zanga a watan Maris, Idris Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa hukuncin zai zama izina ga sauran jama'a wadanda "suke son bin hanya irinta Yahaya"."Lokacin da na ji hukuncin na ji matukar jin dadi saboda hakan ya nuna cewa ba a banza muka yi zanga-zanga ba.

"Wannan hukuncin zai zama darasi ga sauran jama'a wadanda ke ganin za su ci mutuncin addininmu da ma'aikin Allah ba tare da an dauki mataki ba," in ji shi.

Abubuwan da suka kamata ku sani game da kotunan Musulunci

Daga Mansur Abubakar, BBC News, Kano

Jihohi 12 da ke da mafi yawan al'ummar Musulmi a arewacin Najeriya suna aiki da shari'ar Musulunci, amma Musulmi kawai ake yi wa hukunci.

Tsarin Shari'a, wanda yake da kotunan daukaka kara, yana karbar kararraki da suka hada da na aikata laifuka da kuma kananan sabani tsakanin al'umma. Kuma idan ba a gamsu da hukuncin da suka yanke ba akan daukaka kara har zuwa Kotun Koli wacce ba ruwanta da addini.

Alkalan kotunan Shari'a masana ne a fannin dokokin addinin Musulunci da na zamani, ko na bature.

Idan shari'a ta hada Musulmi da wanda ba Musulmi ba, mutumin da ba Musulmi ba yana da damar zabar inda zai kai kara. Kotunan Musulunci suna yi wa wanda ba Musulmi ba shari'a ne kawai idan a rubuce ya amince a yi hakan.

Kotunan Musulunci suna yanke hukuncin da ya hada da bulala, da yanke hannu da kuma kisa.