Abu 10 da coronavirus ta sa ƴan Afirka suka ƙirƙira

A yayin da alkaluman mutanen da suka kamu da korona a nahiyar Afirka ya zarce miliyan guda, masu fasaha a nahiyar sun karɓi ƙalubalen da annobar ta zo da shi ta hanyar ƙirƙiro da hanyoyin samun sauƙi. Ga wasu guda 10 da muka tattaro.

1. ''Likitan mota'' mutum-mutumi

Ɗalibai daga kwalajen fasaha ta Dakar a Senegal sun ƙera mutum-mutumi da ke ayyuka iri-iri domin rage yawan kamuwa da Covid-10 tsakanin marasa lafiya da masu kula da su.

Na'urar na ƙunshe da kamarori sannan ana iya sarrafata ta manhaja. Waɗanda suka ƙirƙire ta sun ce tana iya zirga-zirga tsakanin ɗakunan mutanen da aka killace su auna zafin jikinsu da kai musu magani da abinci.

2. Na'urar wanke hannu mai sarrafa kanta

Bayanan hoto,

Stephen ya samu lambar yabo daga shugaban ƙasa kan abin da ya ƙirƙira

Wani yaro ɗan shekara tara a Kenya, Stephen Wamukota ya ƙirƙiri na'urar wanke hannu mai sarrafa kanta da aka haɗa da katako domin taimaka wa wajen rage yaɗuwar korona.

Na'urar na tsiyayo ruwan wanke hannu ta hanyar taka matakala da aka ƙera a jiki. Wannan ya taimaka wa mutane rage taɓa inda wataƙil za a iya kwasar cutar. Stephen ya samu lambar yabo ta shugaban ƙasa a watan Yuni.

3. Na'urar taimaka wa numfashi ta ventilator

A lokacin da ake fama da ƙarancin ventilator a asibitocin da aka ware don kwantar da masu korona a Najeriya, wani matashi ɗan shekara 20 da ke nazarin ilimin fasaha Usman Ɗalhatu ya yi ƙoƙarin cike wannan giɓi

Ɗalhatu ya ƙirƙiro ƴar ƙaramar na'urar taimaka wa numfashi domin taimaka wa mutanen da ke da buƙatarta - galibin lokuta alamonin cutar korona sun haɗa da ɗaukewar numfashi. Yanzu haka yana shirin ƙera sabbi kamar guda 20.

Bayanan hoto,

Usman Dalhatu ya ce na'urar ventilator ɗins na jiran a amince da ita

4. Takunkumin da aka samar da fasahar 3D

Natalie Raphil ita ce ta samar da wani kamfanin ƙirƙirar mutum mutumi a Afirka Ta Kudu. Tana amfani da fasahar 3D wajen samar da takunkumi 100 a rana domin amfani da shi a asibitocin Johannesburg.

Kusan rabin masu ɗauke da cutar korona a Afrika sun fito ne daga Afirka Ta Kudu.

5. Na'urar wanke hannu da ke aiki da hasken rana

A lokacin da ake tsaka da dokar kulle a Ghana a ƙoƙarin shawo kan yaɗuwar Covid-19, mai ƙera takalmi Richard Kwarteng da ɗan uwansa Jude Osei sun yanke shawarar ƙirƙiro wurin wanke hannu da ke amfani da hasken rana na solar domin inganta tsafta.

Na'urar na sarrafa kanta ta yadda idan ka miƙa hannunka za ta tsiyoyi ruwan haDe da sabulu. Sannan tana ɗaukewa bayan daƙiƙa 25 na wanke hannun - wanda ya yi daidai da daƙiƙoƙin hukumar lafiya ta WHO na wanke hannu.

6. Hanyar gwajin huhu ko X-ray a intanet

Ƙwararru a fannin fasahar ƙere-ƙere sun samar da hanyar gwada lafiyar huhu ko X-ray a intanet wadda ke iya duba ko mutum na ɗauke da cutar korona. Idan mutum ya wallafa gwajin nasa, yana tantancewa da ƙoƙarin gano alamomin ko mutum ya kamu da korona.

Masu bincike a cibiyar binciken kimiyya da fasaha a Tunis sun ce kashi 90 cikin 100 na sakamakon gwaji akwai sahihanci domin yana gano idan mutum ya kamu da cuta.

Har yanzu dai ana sake haɓaka manhajar, sai dai dubban gwajin da aka yi an sanya su a manhajar domin tabbatar da tasirin da Covid-19 ke yi ga huhu.

7. 'Yan sandan mutum-mutumi da ke sintiri lokacin kulle

Hukumomi a Tunusiya sun baza 'yan sandan mutum-mutumi a kan titunan babban birnin ƙasar Tunis a watan Afrilu, don tabbatar da cewa an bi dokokin kulle.

Mutum-mutumin masu sa ido ana kiran su da PGuards, kuma suna sa ido ne kan mutanen da ke tafiya a titi tare da tunkararsu don tambayarsu me ya sa suka fita waje.

Daga nan sai mutum ya nuna katin shaidarsa da sauran takardu ga kamarorin da aka haɗa a jikin mutum-mutumin.

8. Katakon da ke tsaftace kuɗi

Kamfanin dillancin harkokin kuɗi ta hanyar intanet na Danson Wanjohi ya ƙera wata na'ura ta katako da ke tsaftace takardun kuɗi inda ake sanya su a cikinta.

Wanjohi ya samar da na'urar ne ta hanyar sanya mata inji da danƙo da suke bai wa kuɗin damar wuce wa ta cikin na'urar. A yayin da takardun kuɗin ke wuce wa ta cikin na'urar, sai man tsaftace hannu na sanitizer ya ɗiga a kansu ya tsaftace su.

9. Abin gwajin cutar korona cikin minti 65

Wasu ƴan Afrika Ta Kudu masu aiki da kamfanin fasaha Daniel Ndima da Dineo Lioma sun ƙirƙiri kayan gwajin cutar Covid-19 wanda ke samar da sakamako cikin minti 65.

Yawanci dai a kan ɗauki kwana uku kafin sakamakon gwajin cutar korona ya kammala. Sunan kayan gwajin qPCR, kuma akwai wani tsarin fasaha da ake auna ƙwayoyin halttar ɗan adam da shi. Ana buƙatar kayan gwajin su bi matakin hukumomi kafin a amince da su a fara amfani da su.

10. Tsarin bai wa juna tazara a wajen aski

A ƙasar Habasha, masu aski sun ɓullo da wata hanya ta ci gaba da yin sana'arsu bisa bin matakan kare kai daga kamuwa da cutar korona.

Masu aikin kan tsaya ne a wani wani ɗan ɗaki mai kama da irin wanda ake shiga don kiran waya, don ya zama tsakani tsakaninsu da waɗanda za a yi wa askin, inda hakan ke rage barazanar yaɗa cutar a tsakanin mutane.