Ƴan Najeriya a Ghana: Najeriya ta mayar da martani kan yadda Ghana ke rufe shagunan ƴan kasuwarta

Nigeria government/Ghana goment

Asalin hoton, Nigeria goverment/Getty

Ministan harakokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce za su ɗauki matakin gaggawa kan rufe shagunanan ƴan Najeriya a Ghana.

Onyeama ya dauki matakin ne bayan wani hoton bidiyo da ya dinga yawo a intanet wanda ke nuna yadda hukumomin Ghana ke rufe shagon wani ɗan a Accra.

A bidiyon mai shagon ya ce hukumomi sun buƙaci ya biya dala miliyan ɗaya idan har yana son ci gaba da kasuwancinsa a ƙasar

Amma ma'aikatar kasuwanci ta Ghana ta musanta iƙirarin inda ta ce ba ta umurni wani ɗan Najeriya ko ɗan wata ƙasa ba ya biya dala miliyan ɗaya na haraji kafin su ci gaba da yin kasuwanci.

Babban jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar Prince Boakye Boateng ya shaida wa BBC cewa ƴan kasuwa na kasashen waje dole su nuna sun zuba jarin dala miliyan ɗaya a kasuwancinsu a ƙasar.

"A yanzu, wannan shi ne matakin doka, dole ka nuna hujjar ka zuba jarin dala miliyan ɗaya ga kasuwancin da kake, ba wani mun buƙaci a biya harajin dala miliyan ɗaya ba ne ga wani."

Tsohon gwamnan Anambra Peter Obi ya wallafa bidiyo a Twitter inda yake janyo hankali gwamnati ta saurari koken ƴan ƙasarta a Ghana.

Tsarin dokar Ghana ga ƴan ƙasashen waje da suke son kasuwanci

Game da dalilin da ya sa hukumomi suka rufe shaguna a ƙasar, Mista Boateng ya ce saboda ba su cika sharuɗɗn doka ba da ya kamata kafin yin kasuwanci a Ghana. Kuma sharuɗɗan su ne:

  • Yin rigistar kasuwanci a ofishin hukumar da ta dace
  • Tabbatar da kamfani na biyan haraji
  • Dole sai an tabbatar da ingancin kamfani da tabbatar da kayan da yake shigowa da su ba su saɓa ka'ida ba
  • Kamfani dole ya nuna shaidar zuba jarin dala miliyan ɗaya a kasuwancinsu a ƙasar.

Mista Boateng ya kuma faɗi dalilin rufe shagunan wasu ƴan Najeriya;

"Ghana ƙasa ce mai cikakken iko da ke da dokoki, duk da yake ba mu sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta duniya ba."

"Dokar ƙasar nan ta kasuwanci ta Ghana ce kawai, ko kana ɗan Najeriyako Baindiye, bai kamata ka fara kasuwanci ba a kasuwannin Ghana."

Asalin hoton, @nantsng_

Bayanan hoto,

Ƙungiyar ƴan kasuwar Najeriya sun daɗe suna zanga-zanga a Ghana tun 2018

A cewarsa kasuwanci shi ne saye da sayar da kayayyaki. ya ce ƴan kasashen waje za su iya shigo da kaya su zama diloli masu raba kaya amma ba za su iya sayar da kayayyakin ba a matsayin kananan ƴan kasuwa.

Ya ƙara da cewa ba ƴan Najeriya ne kawai suka saɓa dokar kasuwanci ba amma yawancin waɗanda ke kasuwancin a matsayin ƙananan ƴan kasuwa ƴan Najeriya ne.

Shawarwarin ma'aikatar cinikayya ta Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban hulɗa da jama'a na ma'aikatar sadarwa ta Ghana, Prince Boakye Boateng ya ba ƴan kasashen waje shawarwari;

"Shawarwarin da zan ba ƴan uwa na ƴan Najeriya idan na haɗu da su shi ne babu wanda zai hana su yin kasuwancin da ya dace."

"Babu wanda zai hana ƴan kasuwar Afirka shigowa, haɗa abubuwa a tare wuri kamar kantin vory Coast da kantin Najeriya kuma kowa zai haɗu ya yi ciniki.

"Yawancin ƴan kasuwar ƙasashen waje a Ghana kamar; Shoprite da Koala mall da China mall da sauransu hukumomi ba su je sun ɓuakacci su rufe kantinansu ba."

Me ƙungiyar ƴan kasuwar Najeriya a Ghana ke cewa

Asalin hoton, Kwesi Debrah/Joy FM

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shugaban ƴan kasuwar Najeriya a Ghana Cif Kizit suna sane da batun dala biliyan ɗaya na zuba jari amma dukkanin wannan bai fara aiki ba.

Ya ce sun sanar da ƙungiyar Ecowas da gwamnatin Najeriya game da wannan batu tun 2007 da aka fara zancen. Amma a kullum suna cewa wannan dokar ta Ghana ba ta shafi ƴan kasashen Ecowas ba.

"Gaskiyar maganar shi ne idan suna farautar ƴan ƙasashen Ecowas ne, to babu wani ɗan Najeriya da zai ci gaba da zama a Ghana."

"Idan ka zo da dala miliyan ɗaya ka yi rijista, bayan wannan za ka ɗauki ƴan Ghana aiki 25, kuma ba za ka sayar da kaya ba a kasuwanninsu sai dai ka tafi can wajen kasuwa ka sayar a matsayin dila amma ba a matsayin ƙaramin ɗan kasuwa ba."

"Gwamnati kuma ta fayyace cewa ko da ka tafi can wajen kasuwa, duk lokacin da wurin ya samu ci gaba mutane suka fara zuwa suna da damar mayar da wurin a matsayin kasuwa, wanda ke nuna cewa dole ka bar wurin ka fara neman wani wurin na daban."

Mista Kizito ya ce wannan tsare-tsaren ba za su yi wa ƴan ƙasashen Ecowas daɗi ba.

Za a iya tuna cewa wannan ya taɓa faruwa a 2012 da 2018 da kuma yanzu 2020.

"Abin da muke son gwamnatin Ghana da ta fayyace wa ƴan Ecowas shi ne ko wannan dokar ta shafe mu sai mu roƙi gwamnatin Najeriya ta zo ta kwashe mu mu fice daga Ghana domin ba mu da wani zaɓi.