Shari'a kan Rafik Hariri: An samu mutum da laifin kisan tsohon firaministan Lebanon

Vehicles destroyed in the bombing of the armed motorcade of former Lebanese Prime Minister Rafik Hariri, in Beirut, Lebanon, 14 February 2005

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Harin da aka kai a Beirut ya halaka Hariri da wasu mutum 21

Wata kotu ta musamman da ke Netherlands ta samu ɗaya daga cikin mutum huɗu da ake zargi da kisan tsohon Firaministan Lebanon a Beirut cikin shekarar 2005 da hannu a kisan.

Salim Ayyash da sauran mutanen, duk 'yan kungiyar 'yan Shia masu ta-da-kayar-baya ta Lebanon, Hezbollah, sun kasance suna fuskantar tuhuma tun 2014.

Kisan Rafik Hariri, ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasa musulmi a Lebanon ya janyo fushin jama'a a sassan ƙasar.

Hukuncin kotun na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙasar ta Lebanon take cikin rikicin siyasa.

An samu Ayyash da laifin haɗa baki wajen aikata ta'addanci, kisan Hariri da kisan wasu mutane 21 da kuma ƙoƙarin halaka wasu 226 a wani harin ƙunar baƙin wake ranar 14 ga watan Fabrairu.

Ayyash da sauran mutum uku - Hussein Hassan Oneissi, Assad Hassan Sabra da Hassan Habib Merhi - wata kotu ta musamman a Lebanon ta wanke su daga laifin.

Mutum na biyar - Mustafa Badreddine, kwamandan mayakan Hezbollah - an cire sunansa daga cikin wadanda aka zarga bayan an kashe shi a Syria a 2016. Masu shigar da kara sun bayyana shi a matsayin "kanwa uwar gami na shirin da aka kitsa" don kashe Hariri.

Mutanen da aka zarga da kisan tsohon firaministan Lebanon

Salim Jamil Ayyash

Asalin hoton, Special Tribunal for Lebanon

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mr Ayyash yana fuskanta tuhuma biyar, ciki har da hada baki da nufin aiwatar da ta'addancvi, aiwatar da ta'addanci ta hanyar tashin ababen fashewa, da kuma kisan Rafik Hariri da gangan ta hanyar tashin abubuwan fashewa.

Mutumin mai shekara 56 yana da alaka da Mustafa Badreddine ta hanyar aure kuma shi suruki ne ga Imad Mughniyeh, kwamadan kungiyar Hezbollah wanda aka kashe a harin bam na mota a 2008, a cewar bayanan tuhuma.

Kamar sauran wadanda ake zargi, an bayyana Mr Ayyash a matsayin "mai goyon bayan" Hezbollah, saboda masu shigar da kara ba za su iya tabbatar da kasancewarsa mamba a kungiyar ba.

An zargi Mr Ayyash da kitsa kai harin kai tsaye kuma, tare da Badreddine, wanda ya sanya ido kan Rafik Hariri gabanin tashin bam din.

A yayin harin, dan kunar bakin wake ya tashi abubuwan fashewa masu yawa da ya boye a cikin wata motar daukar kaya a yayin da tawagar Hariri ke wucewa ta gaban otal din St Georges da ke Beirut.

An zargi Mr Ayyash da sayo motar, da kuma taka rawa wajen yin karyar daukar nauyin harin da zummar boye hakikanin wadanda suka kai shi.

Lauyoyin Mr Ayyash wadanda kotu ta samar masa sun ce masu shigar da karar sun yi amfani da shaidu muraran, wadanda ba su tabbatar da zargin cewa ya yi amfani da wayoyin hannu ba, wajen tuhumarsa kuma hakan bai nuna yana da hannu a kisan ba.

Hussein Hassan Oneissi

Asalin hoton, Special Tribunal for Lebanon

Mr Oneissi yana fuskantar tuhuma biyar, ciki har da kitsa tuggu domin kai harin ta'addanci ta hanyar amfani da ababen fashewa, da kasancewa da hannu wajen aiwatar da kisan kai da gangan ta hanyar amfani da abubuwan fashewa.

Mutumin mai shekara 46, tare da wanda suka kitsa harin Assad Hassan Sabra, ana zarginsa da hannu wajen zabar wani mutum - Ahmed Abu Adass, wani Bafalasdine da ya samu a masallaci a Beirut - domin ya shirga karya ta hanyar daukar naiyun kai hain, da kuma tabbatar da cewa ya bata. Ba a sake ganin Mr Abu Adass ba tun ranar 16 ga watan Janairu na 2005, lokacin da aka ce ya bar gida domin ganawa da Mr Oneissi.

Masu shigar da kara sun kuma yi zargin cewa Mr Oneissi da Mr Sabra sun yi aiki tare jim kadan bayan harin bam din domin rarraba bayanan karya kan daukar nauyin harin, sannan suka tabbatar an yada bidiyo kan daukar nauyin harin a ofishin gidan talbijin na Al Jazeera da ke Beirut.

Al Jazeera ta samu bidiyon wanda Mr Abu Adass ya ce ya yi niyyar tashin bam da ke jikinsa a madadin abin da masu shigar da kara suka kira kungiyar da ba a santa a zahiri ta mabiya Sunna mai suna "Victory and Jihad and Greater Syria".

Lauyoyin da ke kare Mr Oneissi sun ce masu shigar da kara ba su kawo shaidu gamsassu ba da ke nuna cewa ya kitsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, ko kuma rawar da ya taka wajen batan Mr Abu Adass. Sun kara da cewa masu shigar da karar sun gaza kawo shaidun da ke nuna cewa Mr Abu Adass ba dan kunar bakin wake ba ne.

Assad Hassan Sabra

Asalin hoton, Special Tribunal for Lebanon

Ana zargin Mr Sabra tare da Mr Oneissi da shirya karya wajen daukar nauyin harin.

Mutumin mai shekara 43 yana fuskantar tuhumar aikata laifuka biyar, wadanda suka hada da shirin kaddamar da ta'addanci da kuma kasancewa da hannu wajen kisan kai da gangan ta hanyar amfani da abubuwan fashewa.

Lauyoyin Mr Sabra sun ce shaidun da aka gabatar a kansa ba su na zato ne kuma "suna da rauni matuka", sannan a bayyana take cewa masu shigar da kara ba su iya tabbatar da cewa ya aikata laifi, ko yana da masaniya ko niyyar aikata shi.

Hassan Habib Merhi

Asalin hoton, Special Tribunal For Lebanon

Da fari Mr Merhi ba ya cikin wadanda ake tuhuma. A watan Fabrairun 2014, an gabatar da tuhuma akansa tare da Salim Ayyash da kuma sauran wadanda ake zargi.

Mutumin mai shekara 54 yana fuskantar tuhuma biyar, ciki har da hada baki da nufin aiwatar da ta'addanci da kuma kasancewa da hannu wajen kisan kai da gangan ta hanyar amfani da ababen fashewa.

Aan zarginsa da tsara bayanai na karya kan daukar alhakin hari tare da Mustafa Badreddine, da kuma ganawa da Salim Ayyash domin shirya kai harin.

Masu shigar da kara sun yi amannar cewa Mr Merhi ne ya shirya abubuwan da Hussein Oneissi da Assad Sabra suka tsara na yin karya wajen daukar nauyin kai harin da kuma yada shi a kakafen watsa labarai.

Lauyoyin da ke kare Mr Merhi sun ce masu shigar da kara ba su iya tabbatar da zarge-zargen da suke yi a kansa ba, kuma sun dogara ne kawai da sadarwar da ya yi wadda kuma akwai rauni matuka a cikinta..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Harin da aka kai a Beirut ya halaka Hariri da wasu mutum 21