Rufe iyakokin Najeriya: Ko matakin ya yi amfani bayan shekara ɗaya?

shago a kasuwa
Bayanan hoto,

Rufe kan iyakokin ya sa kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi a kasar

Al'ummomin da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya sun bayyana cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba shekara guda bayan gwamnatin ƙasar ta rufe iyakokinta da ke kan tudu.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin kasar ta rufe iyakokin nata da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake 'yan kasar da dama sun koka kan matakin.

Hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa.

Joseph Attah, kakakin hukumar kwastam na ƙasa, ya shaida wa BBC cewa da Najeriya ba ta ɗauki matakin rufe iyakokin nata wanda ya taimaka wajen inganta noma ba, to da ta fuskanci matsala ta ɓangaren abinci bayan ɓullar annobar korona, da ta tilasta wa ƙasashen duniya rufe ƙofofinsu.

"Harkar noma ta samu inganci, shi ya sa (matakin) ya rage wahalar da ake sha sakamakon zuwa koronabairus.

Asalin hoton, Nigeria Custom Service

Bayanan hoto,

Hukumar Kwastam ta ce rufe iyakokin ya kawo raguwar matsalolin tsaro

Na biyu shi ne ta hanyar tsaro; duk da dai ba a shawo kan (matsalolin) tsaro kwata-kwata ba a Najeriya, amma duk mai hankali ya san cewa abin (yanzu) ba kamar yadda yake da ba," in ji shi.

Sai dai al`ummomi mazauna iyakokin Najeriya, na ganin cewa maimakon Najeriya ta ƙaru da matakin nata, raguwa ta yi. Saboda haka a nasu ra`ayin, garin gyaran gira ne Najeriya ta je, ta rasa ido.

Sada Soli Jibia ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar wasu daga cikin al`umomin Najeriya mazauna kan iyaka, ya ce rufe iyakokin bai yi amfani ba.

'Kowa ya san halin da ake ciki'

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Buhari ya sha jaddada cewa rufe kan iyakokin na taimaka wa manoman kasar

A cewarsa: "Idan an ce an rufe ne saboda kada a shigo da makamai, amma kowa ya san halin da ake ciki a waɗannan yankuna.

Idan kuma an ce an yi don maganar fetur, to ko kwanan nan mun ji an ce an fitar da wasu tankoki wajen ɗari da ashirin da wani abu har wani jami'in kwastam ya rasa aikinsa."

Ya yi kira ga mahukunta su sauya fasali kan rufe iyakokin yana mai cewa ba ƙaramar asara hakan ya janyo ba.

Wani mazaunin kan iyakar Najeriya a jihar Sokoto ya shaida wa BBC cewa rufe iyakokin ya kawo hauhawar farashin kayayyaki a yankinsu.

Sai dai kakakin hukumar kwastan Mr Joseph Attah ya ce jami'ansu da na sauran hukumomin da ke aikin haɗin gwiwa suna bakin ƙoƙarinsu wajen yaƙi da masu fasa-kwauri.

Me mutane suka ce a lokacin da aka rufe iyakokin?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sai dai 'yan Najeriya da dama kuwa na ta korafi kan tsadar kayan abinci da suke tunanin rufe kan iyakokin ne ya jawo

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A bara lokacin da gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta dauki matakin rufe iyakokin kasar ne da nufin dakile ayyukan fasa-kwauri musamman na shinkafa.

To amma wannan mataki ya ja hankalin mutane da dama a kasar tare da jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke goyon baya wasu kuma ba sa goyon baya.

Cikin mutanen da suka magantu a wancan lokacin akwai Sada Soli, dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Kaita da Jibiya a jihar Katsina, kuma a tattaunawar da yayi da BBC, ya ce matakin abin tayar da hankali ne don kuwa zai tsunduma jama'arsu cikin karin matsi.

Shi ma a nsa bangaren Honarabul Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Jigawa, ya ce kamata ya yi a yi shirin yadda ya kamata don kauce wa shigar talaka mawuyacin hali.

Kazaure ya ce ''Muna goyon bayan tsarin gwamnati na dogaro da kanmu, amma bai kamata a dauki matakin rufe iyaka alhalin babu wani tanadi da aka yi wa talaka ba. Idan gwamnati na son daukar matakin sai ta wadata kasa da kayan da za a bukata a kuma saidawa talaka a farashi mai rahusa''.

SHugaba Buhari
Getty
Babu ranar bude iyakokin Najeriya har sai an shawo kan matsalar shigo da kayan da aka haramta a kasar.
Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya

Ita kuwa Kungiyar manoman masara ta Najeriya a lokacin ta ce ta gamsu da yadda farashin masarar da aka noma a kasar ya yi tasiri.

Ta ce bayan rufe iyakokin farashin buhun masara ya koma naira 9,000 wanda a baya ana sayar da shi ne naira 5,000.

Shugaban kungiyar manoman masara a Najeriya, Bello Abubakar Annur Funtuwa, ya ce rufe iyakokin kasar da aka yi da kuma hana bayar da kudin waje da babban bankin Najeriya ya yi ga masu shigowa da abinci a cikin kasar sun taimaka wajen samar wa manoman masara farashi mai kyau.

A nasa ra'ayin a wancan lokacin tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana cewar kasashen da ke mokobtaka da Najeriya ba sa taimaka mata wajen kare tattalin arzikinta.

Sarki Sanusi ya bayyana wa BBC cewar dole ce ta sa Najeriya ta dauki matakin rufe dukkan iyakokinta, domin ta bunkasa tattalin arzikinta musamman abin da ya jibanci noman shinkafa.

Ko a watan Maris din shekarar 2020 gwamnatin Najeriya ta ce 'yan kasar sun ga irin amfanin da rufe iyakokin kasar ya yi a fannin tattalin arzikinta.

Malam Garba Shehu, kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shaida wa BBC hakan, ya jaddada cewa ba za a bude iyakokin kasar ba sai gwamnati ta samu tabbaci daga wurin makwabtanta cewa ba za a su rika yin abubuwan da suka saba wa doka ba a kan iyakokin.

Ya yi tsokacin ne a yayin da Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta aiki da shawarar wani kwamitin bangare uku da ya kunshi Najeriya da Benin da Jamhuriyar Nijar game da rufe iyakokin kasar na tudu da gwamnatinsa ta yi.