'Da hannun kishiya iyaye ke turke 'ya'ya cikin ƙasƙantaccen yanayi'

mace

Wani ƙwararre kan fannin zamantakewa a Najeriya ya yi iƙirarin cewa mafi yawa, kishiyoyi ne ke juya akalar mazan da kan ɗaure 'ya'yansu tsawon shekaru a cikin gida ba tare da kyakkyawar kula ba.

Dr. Usman Abdulƙadir na Jami'ar Usman Ɗan Fodiyo ya ce irin waɗannan magidanta ba sa iya magana a lokacin da ake cutar da 'ya'yan da suka tsugunna suka haifa.

A baya-bayan nan dai, sau uku hukumomi suna kuɓutar da wasu yaran da iyayensu suka garƙame a gidaje cikin mummunan yanayin da bai dace da ɗan'adam ba a jihohin Kano da Kebbi.

Ƙwararren ya ce yawancin yaran da kan shiga irin wannan tasku, uwayensu ba sa gidan. Ya ce: "Ƙila, ko uwayen ba su nan, ko an sallame su, ko kuma, ya zan ƙila yaron mahaifiyarshi ta rasu".

A cewarsa abubuwan da ke faruwa ba yanzu suka fara ba. Irin wannan ƙasƙanta ɗan'adam sun daɗe suna faruwa a ƙasar Hausa.

Dr. Usman ya ce ba hujja ba ce, uba ya tsare ɗansa tsawon shekaru cikin irin wannan yanayi na ƙasƙanci, saboda batun rashin lafiyar ƙwaƙwalwa. "Ai (su) ba asibiti ba ne," in ji shi.

Ya ce da zarar an lura mutum yana da larurar ƙwaƙwalwa, to kamata ya yi mahaifansa su garzaya da shi asibiti amma ba a yi tunanin turke shi ba.

"Don ka ga yaron nan na Kebbi, duk yanayin rayuwarshi ya koma kamar dabba, bai iya tafiya. Ga abubuwa nan da yawa. To, wannan...ƙasƙanta ɗan'adam ne. Gaskiya, wannan bai zama dalili," cewar ƙwararren.

Masanin zamantakewar ya ce idan ma, ana tunanin kangara ce, yaro ke fama da ita, to ai kamata ya yi a binciko sanadin da ya kawo kangarar don magancewa.

Yawancin mazanmu da ke aure, wasu da yawan ba su isa yin aure ba, Dr. Usman ya ce. "In ka ga kangara, yawanci ƙila uwayen sun kasa rainon da Allah ya aza musu".

Ya ce batun tufatarwa da makwanci da sauran buƙatun rayuwa gami da matsin tattalin arziƙin da al'umma take ciki, duk suna da tasiri.

Bayanan hoto,

Iyaye da dama kan ba da hujjar kangarewa a matsayin dalilin tsare 'ya'yansu, wasu kuma su kai gidajen mari

Bugu da ƙari ya taɓo kuma tasirin fina-finai da sauran baƙin al'adu cikin sha'anin tarbiyya, waɗanda a cewarsa sun yi wa al'ummar Hausa illa. "Kuma waɗannan, suna da tasiri kullum".

Ƙwararren ya ce akasarin yaran da iyayensu suka tsare musu buƙatun rayuwa, ba a cika ganin irin wannan kangara a tare da su.

Ba a nan gizo ke saƙar ba, in ji masanin. "Ai kana ganin yara da yawa waɗanda uwayensu ke kula da su sosai, waɗanda suka samu waɗanga abubuwa da aka sharɗanta na aure, da wuya ka ga sun kangare.

Sannan akwai matsalar al'umma. Da, ka ga, ga al'ummarmu yaro na kowa ne, amma yanzu kusan kowa ɗanshi ya sani."

Dr. Usman Abdulƙadir ya ce su ma hukumomi suna da nasu alhaki kan wannan matsala ta turke 'ya'ya da wasu iyayen ke yi. Kamar yadda wasu iyaye suka kasa da unguwanni, su ma hukumomi sun kasa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Matsalolin cin hanci da rashawa kan shafi gidaje

Ya koka kan yadda gwamnoni a yanzu ke yi wa tattalin arziƙin ƙananan hukumomi ƙanshin mutuwa. "Idan kuɗin na yiwowa ƙasa ga irin su ƙananan hukumomi, waɗanga 'yan ƙananan abubuwa duk ana iya riƙe su," a cewarsa.

Ya kuma ce matsalolin cin hanci da rashawa a fannoni daban-daban su ma suna da nasu tasiri cikin sha'anin tarbiyyar 'ya'ya da riƙon gida.

"Cin hanci da rashawa da yai yawa. Cikin harkar ilmi, cikin harkar lahiya, cikin harkar noma. Za ka ga shi na ka sa, hash shi shigo cikin gidajenmu a kasa zama lahiya," masanin ya ce.

Dr. Usman Abdulƙadir ya ce daga cikin mafita kan wannan al'amari, ya kamata ma'aurata su san manufar aurensu da kuma abin da ya kamata su yi bayan sun samu yara.

Na biyu kuma, in ji shi. Dole sai mutane sun tashi tsaye. Duk magidancin da ya kasa riƙe gidansa, to da wuya yaron nan ko yarinya su zama na gari sai dai fa, idan Allah ya kare su.

Ƙwararren ya kuma ja hankali a kan komawa kan halayyar rayuwar al'umma ta baya, lokacin da jama'a ke ganin cewa 'kowa nawa ne'.

"Maƙwabcina, maƙwabcina ne, ɗa nai, ɗana ne. Ɗa na kowa ne. Waɗanda ad da shi, su taimakawa waɗanda ba su da shi. Ba dole sai ta hanyar kuɗi ba, ko ta hanyar tsawatar da yaro ne".