Michelle Obama: An fara babban taron Democrat da taron dangi kan Trump

Michelle Obama.

Asalin hoton, DNC

Bayanan hoto,

Michelle Obama.

An fara gudanar da babban taron jam'iyyar Democrat da aka jima ana dako a Amurka.

Mutane da dama sun gabatar da jawabansu a yayin taron da ake gudanarwa ta bidiyo, fitattu daga ciki sun hadar da daya daga cikin jiga-gigan jam'iyyar Bernie Sanders, da tsohuwar matar shugaban kasar Barack Obama wato Michelle Obama.

Mr Sanders wanda ya tsaya takarar shugaban kasa tare da Joe Biden ya bukaci dukkanin magoya bayansa su goya wa Biden baya.

Ya bayyana mulkin shugaba Trump na jam'iyyar Republican a matsayin ''mulkin mallaka''

Jawabin da ya fi jan hankali shi ne na matar tsohon shugaban kasar Barack Obama wato Michelle Obama, wadda ta shafe tsawon mintuna 20 ta na bayani cikin takaicin abin da ta ce yana faruwa a Amurka.

''Ni ba yar siyasa ba ce, kuma kun san na tsani siyasa, ina fada muku gaskiyar abin da ke raina ne, cewa Trump ya nuna ba zai iya mulkarmu ba, halin da muke ciki ya saba da dadadden mafarkin da muka jima muna yi na barwa yayanmu da jikokinsu gobe mai kyau''in ji ta.

Asalin hoton, DNC

Bayanan hoto,

Joe Biden yayin tattaunawa da wasu Amurkawa yayin taron

Za a shafe kwanaki hudu ana gudanar da taron, da ake sa ran manyan yan jam'iyyar Democrat da dama za su gabatar da nasu jawaban.

Wasu daga cikinsu sun hadar da tsaffin shugabannin kasar Barack Obama, da kuma Bill Clinton.

Tsohuwar 'yar takarar shugaban kasa da ta kara da Trump a 2016 wato Hillary Clinton za ta gabatar da nata jawabin ita ma.

A ranar Alhamis da za a kammala taron ne mai neman jam'iyyar ta tsayar da shi takara Joe Biden, da mataimakiyarsa Kamala Harris za su karbi tikiti.

Me Michelle Obama ta ce?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mrs Obama, wacce ta nadi jawabin da za a ta gabatar tun kafin Mista Biden ya sanar da wacce za ta zama mataimakiyarsa, Sanata Kamala Harris, kwana shida da suka gabata, ta ragargaji Mr Trump sosai a ciki.

''Ba za ka zo haka kawai ka nemi wannan kujerar ba bayan ba ka dace da ita ba,'' kamar yadda ta fada a jawabin da ya kawo karshen taron na ranar Litinin.

Ta ci gaba da cewa: ''Tattallin arzikinmu yana cikin halin ha'u'la'i saboda kwayar cutar da wannan shugaban kasar ya ki ba ta muhimmanci ba tsawon lokaci.''

''Sannan kuma ga yadda batun fafutukar muhimmancin ran bakaken fata ya dinga samun cikas daga ofishinsa,'' in ji Mrs Obama.

''Saboda a duk lokacin da muka kalli Fadar White House da batun shugabanci, ko neman sassauci kan wani batu, to sai dai a samu cikas da rabuwar kai da nuna halin ko in kula daga fadar a ko yaushe.''

Ta ce shekaru hudun da suka gabata za su yi matukar wahala wajen yi wa yaran Amurka bayaninsu.

''Suna ganin yadda shugabanninmu suke nuna cewa wasu 'yan kasa makiyan kasar ne, amma kuma ake bai wa fararen fata fifiko.