Birnin Wuhan: Kalli yadda ake shakatawa a garin da coronavirus ta samo asali

Wuhan swimming pool 15 August

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dubban mutane cunkushe wuri guda a bikin kade-kade da aka shirya a Wuhan

Dubban mutane sun taru kafaɗa da kafaɗa ba tare da takunkumin fuska ba, suna ta wasa da balam-balam din zama a cikin ruwa tare da yin shewa a wani bikin kaɗe-kaɗe.

Ba wai shi ne hoto mafi shahara a 2020 ba, amma abu ne da ya ja hankali a karshe mako a birnin Wuhan, inda Covid-19 ta samo asali a bara.

Hotunan da aka wallafa ana bikin rakashewa a wurin shakatawar Maya Beach da ke Wuhan - alamomi da ke nuna wannan yankin ya fita daga kangin da duniya ta shiga na yaki da cutar korona - yanzu ya zama tarihi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babu wanda ya sanya takunkumi ko bai wa juna tazara a wannan biki

Hotunan sun sha bamban da abin da duniya ta gani a lokacin da Wuhan ta shiga kullen annobar cutar korona a watan Janairu - birnin da ya koma kamar an yi sharar titin babu mutane ballantana ababben hawa.

A watan Afrilu aka dage dokar kulle kuma ba a samu yaduwar cutar tsakanin 'yan gida ba a Wuhan ko lardin Hubei tun tsakiyar Mayu.

Farfadowa sannu a hankali

Wuhan ta shiga yanayin dokar kullen da ba a taba gani ba a ranar 23 ga watan Janairu - a lokacin da cutar ta kashe mutum 17 da shafar sama da 400.

Sai bayan mako guda sannan China ta tabbatar da cewa cutar na yaduwa tsakanin mutane, wanda ba a taba ganin irinsa ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akwai lokacin da birnin Wuhan ya kasance tamkar an share al'ummarta lokacin dokar kulle

Birnin mai yawan al'umma miliyan 11 sai da ya kasance an ware shi daga sauran yankunan China, bayan gano dubbai sun kamu a cikin watanni kalilan da kebe mutane. An soke taron mutane da yawa da umartar mutane su yi nesa-nesa da juna.

A watan Maris aka soma sasauta dokar kullen.

Mutum guda a kowane gida ake bai wa damar fita waje na akalla sa'a biyu.

Kantunan sayayya sun sake soma budewa, hada-hadar ababen hawa na dawowa sannan mutane sun soma fitowa kadan-kadan - ko da yake an ci gaba da mutunta dokar bai wa juna tazara da sanya takunkumi.

A ranar 8 ga watan Afrilu, aka dage dokar kulle a Wuhan a hukumance.

Masu son aure sun gaggauta ganin an yi bikinsu, bayan tilasta musu da cutar ya yi na dakatar da shirin bikinsu a tsawon watannin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'aurata sun yi bikin aurensu a birnin Wuhan bayan dage dokar kulle

An kai wani lokaci da abubuwa suka kasance suna dawowa sannu a hankali yayin da aka bude makarantu, an mayar da da hada-hadar kasuwanci sannan motocin haya sun dawo aiki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daliban ajin karshe a makarantun sakandare sun koma makaranta tun watan Mayu

A ranar 12 ga watan Mayu, an samu sabbin mutum shida da suka kamu da korona. Birnin ya kudiri anniyar matakan gwaji ga illahirin mazauna garin miliyan 11. Daga baya an shawo kan barkewar annobar.

A watan Yuni, kasuwannin dare - da ke ci a manyan tittuna - an ba su izinin sake budewa.

Bayan wata guda, a watan Yuli, rayuwar ta soma komawa daidai a yankuna da dama na China. An bude sinimomi a galibin yankunan, wuraren wasa da wurin karatu da gine-ginen adana kayan tarihi. Sannan mutane na dawo da gudanar da taruka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yadda ake kallon fim a wata sinima da ke Wuhan

A yau, alamu sun nuna cewa rayuwa ta dawo yadda take a baya a Wuhan. Hotunan mutanen da suka halarci tare da rakashewa a bikin HOHA a karshen mako ya tabbatar da maganar da ake yi.

Akwai kungiyoyi da kamfanonin da ke bai wa mata masu sha'awar zuwa yawon bude ido rangwamen tiketi a kokarin jawo hankulan baki.

Tun 25 ga watan Yuni aka bude wurin wasan Theme Park amma sai a watan Agusta aka soma samun baki da ke kai ziyara.

Wurin wasan da shakatawa a yanzu na karbar baki dubu 15 a kowane mako, a cewarsa, kusan rabin adadin mutanen da ya karba a irin wannan lokaci a bara.

A shafukan sada zumunta a China, masu tsokaci sun nuna mamakinsu kan yadda aka amince da shirya irin wannan katafaren taron a Wuhan. An ta nuna damuwa a Twitter da Facebook.

Sai dai a Wuhan ba a samu barke korona a cikin gida ba tun tsakiyar Mayu, sannan mutum miliyan 9.9 aka yi wa gwajin cutar a birnin. Babu haramci da ke aiki yanzu haka kan taron jama'a.

Bayanan bidiyo,

Wane sauyi Wuhan ta samu? Me kuma duniya za ta koya daga wajensu bayan janye dokokin kulle?

A wani bangare kuma, cutar na ci gaba da karuwa a wasu yankunan. Akwai sama da mutum miliyan 21 da ke dauke da cutar a fadin duniya.

Kasashe irinsu New Zealand da Koriya Ta Kudu - da suka yi nasarar shawo kan cutar - yanzu haka suka fuskantar barazanar sake barkewarta.

Don haka zai dauki tsawon lokaci kafin hankulan kasashe ya kwanta da aminta da shirya taruka.

Dukkan hotunan na da hakkin mallaka