Ciwon suga: Shin akwai alaka tsakanin shan sukari da cutar?

  • Buhari Muhammad Fagge
  • Broadcast Journalist
sugar

Asalin hoton, Getty Images

Da yawa a yankin kasashen nahiyar Afrika na ganin sukari wanda a Ingilishi ake kira (White Sugar) na da alaka da ciwon suga (Diabetes).

Masana na cewa wannan ciwo ne da aka fi gado a mafi yawan lokaci - duk da yake a wasu lokutan kuma ko mutum bai yi gado ba, yana iya kamuwa da shi.

Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa wani kwararran likita ne da ke Abuja, ya bayyana wannan cuta a matsayin gazawar wani sinadari da ake kira (Insulin) ko kuma rashin sinadarin baki daya a jiki, wanda aikinsa shi ne tunkuɗa sugan da ke cikin jinin mutum zuwa in da ya kamata ya je.

Nau'o'in Ciwon Suga

1. Akwai nau'in farko da ake kira Type 1- wanda mutanen da ba su gaji ciwon ba daga zuri'arsu ke fama da shi.

An fi samunsa a jikin kananan yara ko kuma daga kan 'yan shekara 20 zuwa kasa.

Masu wannan nau'in su ne mafi karanci a duniya, "domin yawansu bai wuce miliyan daya da digo biyu ba a duniya baki daya," in ji Dakta Salihu Kwaifa.

Masu wannan nau'in su ba su da sinadarin Insulin duka a jikinsu, kuma za a ga alamun suna dauke da ciwon saboda suna zuwa da rama da yawan fitsari da yawan jin ƙishirwa da kuma yawan shan ruwan, kamar yadda likitan ya zayyana.

Asalin hoton, Dr Kwaifa

Bayanan hoto,

"Abin da ya kamata mutane su sani shi ne ciwon-suga ba ciwo ba ne da ake iya yadawa wani," in ji Dakta Salihu

2. Akwai nau'in Type 2 - wannan nau'in ya fi yawa tsakanin mutane, ya fi addabar mutanen da ke tsakanin shekara 20 zuwa 79.

Masana na cewa akwai akalla akwai masu fama da cutar a duniya fiye da mutum miliyan 560.

Jin laulayi na daga cikin alamun wannan nau'in duk da cewa a wasu lokutan yana sanya rama da kuma jin yunwa shi ma, yawan fitsari da yawan shan ruwa alamomi ne da suka fi zama gama-gari ga masu wannan cuta.

Wannan nau'in ya fi yawa a bangaren gado - yana yawan bin zuri'ar mutane, daga uwa ko uba ko baffa da dai sauran dangi.

Abubuwan da suke janyo ciwon-suga ga wadanda ba su gada ba

Dakta Salihu ya jero wasu manyan abubuwan da suke kara hadarin kamuwa da wannan cuta musamman da wadanda ba su gaje ta ba daga kowa, ga wadanda suka gada kuma in aka samu wadannan abubuwa sai su kara ta'azzara cutar.

1- Kiba: kiba na daga cikin abubuwan da suke janyo wannan cutar, nauyi da tsayi su wuce misali.

2- Rashin motsa jiki: Abu ne mai amfani ga wadanda suke yi in da dama a kullum mutum ya motsa jikinsa na akalla minti 30, kuma ya zama yana yin haka sau hudu a mako. Ba dole ba ne sai an yi minti 30 din a lokacin guda amma yana da matukar muhimmanci a rika motsin.

3- Cin abinci mai yawan suga: Abincin da suke da sinadarin (glucose) cikinsu, wanda shi wannan sinadari ana masa kallon ciwon-siga ba ki daya. Abinci kamar fura ko tuwo ko waina ko shinkafa ko rogo da sauransu. Ba cin abincin ba ne ke da matsalar, a'a rashin motsa jikin shini hadari.

Alakar da ke tsakanin sikari da ciwon-suga

Asalin hoton, Hajiya Maijidda

Bayanan hoto,

Malama Maijidda Badamasi Burji ta ce akwai alakar sikari da ciwon-suga amma ba ta kai tsaya ba ce

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Malama Maijidda Badamasi Shu'aibu Burji wata kwararriya ce kan harkokin abinci da cutukan da ke da alaka da abincin kai tsaye, ta ce akwai alakar sikari da ciwon-suga amma ba ta kai tsaya ba ce.

Idan akwai wannan mummunar lalura mai kisa, da ta hadu da wanda ba ya lura da yadda ake shan sikari sai ka ga ta kara ta'azzara cutar.

Shi akan kansa ba ya kawo cutar ciwon-siga sai dai ya kara wa cutar muni.

Kungiyar Lafiya Ta Amurka ta ba da shawarwari kan cewa, dan shekara hudu zuwa shida ba a son ya sha sikari sama da cokali biyar ko kuma kwaya biyar ta sikari mai iyali.

Dan shekara ko 'yar shekarar 7 zuwa 10 kar ya wuce cokali shida na shayi kwatankwacin giram 24, daga shekarar 11 zuwa manya wadanda ba su wuce kilo 30 cokali bakwai ya fi dacewa su sha a rana.

Sai namiji babba lafiyayye cokali tara ya kamata ya sha kwatankwacin giram 38 a rana yayin da babbar mace aka shawarce ta da ka da ta sha sama da cokali shida daidai da giram 25.

Amma ba a fadi adadin da masu wannan cuta ya kamata su rika sha ba a rana, saboda ko wanne da irin yadda matakin cutar yake a jikinsa.

Da wadannan shawarwari za a iya samun takaitar hadarin wannan cuta, kama daga wanda yake da ita ko wanda ya ke da yiyuwar daukarta.

Bayanan sauti

Hira da Dr Mijinyawa kan tsadar maganin ciwon suga

Shin ana warkewa daga wannan cuta?

Masana a fannin kiwon lafiya sun ce ba kasafai ake warkewa tas ba, sai dai akan iya samun saukin da akan mantawa da cewa wane yana da cutar ciwon-suga.

Ana iya kiyaye wannan cuta ne ta hanyar kaurace wa abubuwan da kan iya ta'azzarata, da kuma wadanda ke samar da saukin ciwon.

Asalin hoton, Dougal Waters

Abincin da yake da (Fiber) wato mai hade da dusa wanda ba a cashe ba shi ne na farko da ya kamata a ce mara lafiyar ciwon-suga na mayar da hankali a kai.

Hakanan nau'in ganyaye irinsu alayyahu da gurji da karas latas da dai sauransu, sai 'ya'yan itace da su ma suna matukar taimakawa wajen kwantar da wannan cuta a jikin dan adam.

"Abin da ya kamata mutane su sani shi ne ciwon-siga ba ciwo ba ne da ake iya yada wa wani" in ji Dakta Salihu Kwaifa.