Juyin mulki a Mali: Halin da aka shiga a Mali bayan sauke Ibrahim Boubacar Keita

Malian soldiers are celebrated as they arrive at the Independence Square in Bamako, Mali - 18 August 18, 2020.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Faransa ta bukaci sojoji su koma bariki

Gwamnatin Najeriya ta nuna rashin jin daɗinta bisa juyin mulkin da sojojin Mali suka yi wa Tsohon Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta.

A wata sanarwa da ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya fitar, ya ce gwamnatin Najeriyar na buƙatar a dawo da tsarin mulkin dimokraɗiyya cikin gaggawa a ƙasar.

Ministan ya ce gwamnatin Najeriyar na maraba da matakin ko ta kwana da ƙungiyar ECOWAS ta ɗauka kan ƙasar ta Mali.

A ranar Talata ne dai sojojin ƙasar Mali suka tilasta wa Tsohon Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta yin murabus.

Sojojin da suka hamɓarar da Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta sun bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin gudanar da sabon zaɓe a ƙasar.

Wannan ya biyo bayan bayyanar shugaban a kafar talabijin, inda ya ce ya sauka daga muƙaminsa.

Sojojin sun yi awon gaba da shi tare da firaministansa daga babban birnin ƙasar zuwa wani sansanin soja.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta AU da Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

Tuni itama ƙungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin daɗinta bisa wannan lamarin, inda ta ce ta dakatar da ƙasar ta Mali daga cikin ƙungiyar ta ECOWAS.

ECOWAS ɗin a wata sanarwa da ta fitar, ta ɗauki aniyar rufe duka iyakokin ƙasar ta Mali, (na sama da ƙasa), da kuma dakatar da kasuwanci da cinikayya tsakanin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS da kuma Mali.

Shi ma Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda a baya ya yi tsayuwar daka wurin ganin cewa an samu sulhu a ƙasar ta Mali, ya ce bai da wani abin da zai ce kan lamarin da ya faru a Mali, sai dai kawai yana tare da matsayar da ƙungiyar ECOWAS ta ɗauka.

Mai magana da yawunsa ne ya shaida wa BBC hakan da aka nemi jin ta bakin Tsohon Shugaba Jonathan ɗin.

Tun da farko dai, Shugabannin rundunar sojojin Mali sun bayar da umarnin rufe iyakokin ƙasar tare da sanya dokar hana fita da dare, a cewar wata sanarwa da mataimakin shugaban ma'aikatan sojojin sama na ƙasar.

"Daga yau, 19 ga watan Agustan 2020, an rufe dukkanin iyakoki na sama da na ƙasa har sai baba ta gani. An saka dokar hana fita daga ƙarfe 9:00 na dare zuwa 5:00 na asuba har sai baba ta gani," in ji Kanar-Manjo Ismaël Wagué a wani jawabin talabijin.

Shugaba Keita ya sauka daga mulki

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya yi murabus daga mulki, bayan sojoji sun tsare shi a ranar Talata, kamar yadda gidan talbijin ɗin ƙasar ya ruwaito.

A wani jawabi da aka yaɗa ta kafar talbijin, Ibrahim Keïta ya ce ya kuma rusa gwamnatin ƙasar da majalisar dokoki.

Ya ƙara da cewa: "Ba na son a zubar da jini don ganin na ci gaba da mulki".

Al'amarin na zuwa ne bayan sojoji sun ɗauke su, shi da Fira Minista Boubou Cissé zuwa wani sansanin soji da ke kusa da babban birnin ƙasar Bamako, abin da ya janyo Allah-wadai daga ƙasashen yankin da kuma Faransa.

Ana nuna fushi a tsakanin dakarun sojin ƙasar dangane da biyan haƙƙoƙin aiki da kuma ka batun ƙazancewar faɗa da masu iƙirarin jihadi - da kuma gagarumar rashin jituwa da tsohon shugaban ƙasar.

Shugaba Keïta ya lashe zaɓe wa'adi na biyu a shekara ta 2018, sai dai al'umma na nuna fushi game da cin hanci da rashawa da kuma rashin iya gudanar da harkokin tattalin arziƙi da ƙaruwar tarzomar ƙabilanci a yankunan ƙasar.

Lamarin ya janyo manya-manyan zanga-zanga a karo da dama cikin watannin baya-bayan nan.

Wani sabon ƙawancen 'yan adawa ƙarƙashin jagorancin jagorar addinin Musulunci, Mahmoud Dicko, ya yi kira a yi garambawul bayan ya yi watsi da sassaucin da Ibrahim Keita ya yi wanda ya haɗar da kafa wata gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Me Mr Keïta ya ce?

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A shekara ta 2018 Ibrahim Boubacar Keïta ya lashe zabe a karo na biyu

Mr Keita ya sanar da yin murabus ɗinsa a wani jawabi da ya gabatar a gidan talbijin yana sanye da takunkumi yayin da ake tsaka da fama da annobar cutar korona.

''Idan a yau wasu daga cikin dakarun sojinmu na son kawo ƙarshen wannan abu ta hanyar shigarsu cikin lamarin, ina da wani zaɓi?'' ya tambaya.

''Ba na ƙin kowa, soyayyata ga ƙasata ba za ta bar ni na yi haka ba,'' kamar yadda ya faɗa. ''Allah Ya cece mu.''

Me sojojin suka ce?

An karanta wani jawabi a talabijin ranar Laraba da sassafe a madadin wani kwamitin ceto ƴan ƙasa na National Committee for the Salvation of the People.

Mataimakin shugaban rundunar sojin sama Col-Major Ismaël Wagué ya ce: "Muna gayyatar ƙungiyoyin fararen huka da masu fafutuka na siyasa da su zo mu haɗa kai don ƙirƙirar sabin yanayi na miƙa mulki ga farar hula inda za a yi sahihan zaɓuka ta hanyar bin tsarin da ya dace wajen sanya harsashi don gina sabuwar Mali''.

Ya ƙara da cewa: ''Daga yau 19 ga watan Agustan 2020, an rufe dukkan iyakokin sama da na ƙasa har sai yadda hali ya yi. Sannan dokar hana fita ta fara aiki daga ƙarfe 9 na dare zuwa 5 na asuba (agogon ƙasar) har sai yadda hali ya yi.'

Kanal Wagué ya ce: "Ƙasarmu na nutse wa cikin rikici da rashin bin doka da rashin tsaro duk gaibi saboda laifin mutanen da makomarta ke hannunsu.''

An yi harbe-harbe a kusa da sansanin soji a Mali

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

'Yan Mali sun yi wa sojojinsu sowa lokacin da suka shiga Bamako

Tun da farko dai a ranar Talata wani mai magana da yawun rundunar sojin Mali ya tabbatar da cewa an yi harbe-harbe a cikin wani sansanin sojin da ke babban birnin kasar Bamako.

Ofishin jakadancin Norway ya ce ya samu bayanai cewa dakaru suna kan hanyarsu ta zuwa babban birnin kuma ofishin jakadancin Faransa ya bayar da shawrar cewa mutane su zauna a gida.

Hakan na zuwa ne a yayin da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta yake fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mulki inda ake yin zanga-zangar adawa da shi.

Ana ci gaba da samun fushi daga 'yan kasar kan munin da lamarin tsaro ke yi inda rikice-rikicen 'yan ta'adda da na kabilanci ke ta karuwa.

Mutane suna kuma yin korafi kan karuwar cin hanci da tabarbarewar tattalin arziki.

Me muka sani game da boren sojoji?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An ga sojoji na sintiri a kan tituna bayan an ji amon bindigogi

Bayan samun rahotannin harbe-harben ne kuma sai sojoji suka ƙwace iko da ƙasar tare da kama da tsare Shugaba Keita a ranar Talatar, da ma wasu sauran manyan 'yan majalisarsa a wani abu mai kama da juyin mulki.

Sojojin juyin mulkin sun ƙwace iko da sansanin Kati.

An yi ta samun ɓacin rai daga ɓangaren sojoji kan biyansu da kuma ci gaba da rikici da ake yi da masu ikirarin jihadi - da kuma nuna adawa da Shugaba Keita da ake ta yi a ƙasar.

Juyin mulkin na ranar Talata dai ya jawo Allah-wadai daga ƙasashen duniya.

Wani soja Kanal Malick Diaw - mataimakin kwamandan sansanin soji na Kati - da kuma wani kwamanda Janar Sadio Camara ne ke jagoranatar bore, Kamar yadda wakilin BBC Abdoul Ba a Bamako ya ruwaito.

Bayan ƙwace sansanin ne, mai nisan kimanin kilomita 15 daga Bamako, masu boren sun yi maci zuwa babban birnin, inda sowar cincirindon mutane ta yi tarbe su.

Mutanen da suka taru sun buƙaci Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ya sauka daga mulki.

Bayanan hoto,

Rikicin kasar Mali ya dade yana ruruwa shi ya sa mutane ba su yi mamaki ba da aka ture gwamnatin Keita

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kungiyar kasashen Yammacin Afirka, Ecowas da kasar Faransa sun yi tir da harbe-harben da sojojin suka yi a wani sansaninsu.

Kakakin gwamnatin kasar Yaya Sangare ya tabbatar wa BBC Afrique cewa an kama shugaban kasa da Firaminista.

Ibrahim Boubacar Keïta yana gidansa da ke Sebenikoro, Bamako, lokacin da sojojin da suka yi tawaye suka kama shi da misalin karfe 4.30 na yamma a agogon kasar.

Yana tare da Firaiminista, Boubou Cissé, da dansa, da mataimakinsa Karim Keïta.

Rahotanni sun ce ɗan shugaban ƙasar da shugaban Majalisar Dokokin Mali da ministocin kuɗi da harkokin waje na daga cikin sauran jami'an da sojoji suka tsare.

Ba a iya fayyace adadin sojojin da suka shiga cikin bore ba.

Sansanin soji na Kati ya taɓa jan hankula lokacin wani boren sojoji a shekara ta 2012, bayan dakarun ƙasar sun yi fushi a kan gazawar manyan kwamandojin Mali wajen dakatar da masu iƙirarin jihadi da kuma Azbinawa 'yan tawaye sun ƙwace iko da arewacin ƙasar.

Ci gaba da zanga-zanga

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tun makon da ya gabata aka ci gaba da zanga-zanga bayan Babbar Sallah

Da ma a ranar Talata kungiyoyin 'yan adawan kasar sun sha alwashin ci gaba da gagaruman zanga-zanga, inda za a yi babban maci a ranakun Juma'a da Asabar.

Wakilan kungiyoyin June 5 Movement (M5) sun ce sun sanya ɗan bar yin zanga-zangar adawa da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta.

An shirya yin zanga-zanga da dama a wannan mako ciki har da maci na mata.

'Yan adawar sun ɗauki hutun zanga-zangar a lokacin bukukuwan Sallar Layya, sai kuma suka dawo da ita a ranar Talata amma an yi ta tarwatsa su da hayaƙi mai sa hawaye.

'Yan adawar sun zargi gwamnati da alhakin tabarbarewar tattalin arziki, da kuma ƙaruwar cin hanci baya ga kasa cimma yarjejeniya tsakaninta da 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Kokarin kasashe maƙwabta na sasantawa ya gaza aiki, inda 'yan adawa suka ƙi yarda da yin sulhu matuƙar ba shugaban ne ya yi murabus ba.

Wasu labaran da zaku so karantawa