Kyautar Emmy: Kiki Mordi, ma'aikaciyar BBC da ta fallasa malamai kan lalata da ɗalibai za ta samu yabo

Kiki Mordi

Asalin hoton, TWITTER/@kikimordi

Bayanan hoto,

'Yar jarida ce ta yi badda-kama a matsayin daliba yar shekara 17

Shafin Twitter a Najeriya ya kaure da yabo da kuma jinjinawa ga matashiyar 'yar jaridar nan, Kiki Mordi, wacce ta jagoranci shirin BBC Africa Eye na #SexForGrades da ya bankado irin lalatar da malaman jami'a ke yi ga dalibansu kafin su bari su ci jarrabbawa.

Hakan ya faru ne kuwa bayan an sanar da sunan 'yar jaridar a cikin wadanda ke takarar samun lambar yabo mai daraja ta Emmy.

A bara ne Kiki Mordi ta nadi bidiyon wasu malaman jami'a, ciki har da na jami'ar Lagos, Dakta Boniface Igbeneghu, bayan ta yi badda-kama a matsayin daliba da ke son ya taimake ta don ta samu gurbin karatu.

Bayanan bidiyo,

Yadda malaman jami'a ke lalata da 'yan mata - binciken kwakwaf na BBC

Malamin ya nuna cewa zai iya taimakonta ne kawai idan ta yarda ta yi jima'i da shi.

Bayan fitar bidiyon ne Jami'ar Lagos da kuma Cocin The Foursquare Gospel Church a Najeriya, wadda yake matsayin fasto, suka raba gari da Dakta Igbeneghuta.

Yanzu dai an sanya ta cikin wadanda ka iya lashe lambar yabo ta Emmy, wadda ake bai wa mutanen da suka nuna wata bajinta ta hanyar wani labari da aka watsa a talbijin.

Galibin wadanda suka yabe ta sun jinjina mata kan namijin kokarinta wajen bankado wannan badakala ta #SexForGrades.

Ayo Sogunro, wani fitaccen mai amfani da Twitter, ya ce ya yi murna sosai ganin cewa Kiki Mordi za ta iya lashe lambar Emmy duk da sukar da ake yi mata a shafin Twitter:

Ita kuwa Ebele cewa ta yi shirin BBC Africa Eye da ya bankado #SexForGrades ya cancanci samun wannan lambar yabo.

"#SexForGrades ya cancanci wannan [lambar yabo]. Saboda abubuwan da ya tono, da kuma samar da tsaro, da tabbatar da doka, da cin hancin da ya bankado kuma yake ci gaba da bankadowa... Kiki gwarzuwa ce."

A yayin da miliyoyin mutane a duniya suka dade da sanin lambar yabo ta Emmy, ita kuwa Hecallsmemilan ta ce ba ta taba jin labarinta ba sai yanzu da aka sanya Kiki Mordi cikin wadanda ka iya lashe ta.

"Ban taba jin wannan lambar yabo ba kafin yanzxu. Allah Ya yi wa Kiki albarka saboda ba su damar haskakawa."

A gefe guda kuma, Fisayo Longe, ta caccaki mazan da ke zagin Kiki tana mai cewa yanzu ya kamata su san cewa ita ba sa'arsu ba ce.

Kuka da dariya

Kiki Mordi ta shaida wa BBC Hausa cewa ta yi matukar jin dadi da aka sanya sunanta cikin wadanda za su iya lashe lambar yabo ta Emmy.

Matashiyar 'yar jaridar ta ce ta ji kamar za ta yi kuka amma ta fashe da dariya lokacin da ta samu lamarin cewa an sa sunanta cikin mutanen da za su iya cin lambar yabo.

"Na ji tamkar zan yi kuka, amma na fashe da dariya. Na ji matukar dadi da cewa wannan batu na cin zarafin mata ya ja hankalin duniya. Fatana yanzu shi ne, majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudurin dokar da zai hukunta duk wanda aka samu da laifin yin lalata da dalibai," in ji ta.