Shan gahawa mara yawa kan taimaka wa masu ciki

pregnant woman drinking coffee

Asalin hoton, Getty Images

Yayinda ya kamata a ce mata masu ciki da kuma matan da ke kokarin ganin sun samu juna biyun sun rage yanayin yadda suke shan gahawa, masana sun bayyana cewa shan kofin shayi ko na gahawa kadan a rana ba shi da wata matsala.

Bayanan na su na zuwa ne bayan da wata sabuwar kasidar bincike kan kiwon lafiya ta yi hasashen cewa babu wata iyaka kan abubuwan da za a kiyaye a juna biyu.

Amma kuma masanan sun ce wannan bayanan ta da hankali ne .

Hukumar kula da kiwon lafiya ta Burtaniya NHS da karin wasu kungiyoyi sun ce bai kamata shan miligiram 200 ko kasa da haka ya zama wata barazanar a zo-a-gani ba game da girman jariri a ciki ko kuma bari yayin da yake cikin mahaifa ba.

Wannan kasidar bincike mai cike da takaddama, da aka wallafa a mujallar BMJ Evidence Based Medicine, ta duba bincike guda 48 da aka gudanar a kan batun.

Marubucin wannan kasida, Prof Jack James, wanda masanin halayyar dan adam ne a jami'ar Reykjavik a kasar Iceland, ya amince cewa sakamakon binciken ya dogara ne a bisa tattara bayanan wasu al'umma a wasu yankuna kebantattu, don haka babu tabbacin cewar lallai ne shan gahwa da dangoginta ka iya zama hadari ga masu juna biyu.

Amma kuma ya bayyana cewa binciken na sa wanda ya danganta shan gahawa da hadari, ya nuna cewa kaurace wa shan shayi ko gahawa gabaki daya muhimmiyar shawara ce ga mata masu juna biyu da ma matan da ke kokarin ganin cewa sun samu cikin.

Wasu masanan da ke jayayya a kan sakamakon binciken sun ce wuce makadi da rawa ne.

Kamar yadda hukumar ta NHS ta bayyana, hukumar lura da inganci abinci ta kasashen Turai da kuma kwalejojin nazarin kula da lafiyar yara da mata masu juna biyu na Amurka da Burtaniya sun amince cewa a amma ba a daina shan gahwa gabaki daya ba yayin juna biyu.

Dr Luke Grzeskowiak, wani masani a fannin harhada magunguna a jami'ar Adelaide da ke kasar Australia, ya ce, kasidar binciken abin tayar da hankali ne mai kuma cike da rashin wata kwakkwarar madogara.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Akwai ka'idojin da ke da alaka da batun da ya shafi juna biyu, amma kuma abun da bai kamata a ce yana ciki ba shi ne haddasa duk wata fargabar babu gaira babu dalili. Daga karshe, a tabbatar wa da mata cewa za su iya shan gahawa da dangoginta saisa-saisa a lokacin da suke dauke da juna biyu.

Farfesa Andrew Shennan, masani kan kula da lafiyar yara da ke Kings College London, ya ce wasu daga cikin abubuwan da binciken ya kunsa ka iya kasancewa akwai kura-kurai ne saboda binciken ya dogara ne ga bayanan da aka tattara daga matan da suka kudiri daina shan gahawa da dangoginta.

Haka kuma ya kara da cewa yana da matukar wahala a cire sauran abubuwan da ke da hadari da mai yiwuwa masu shan shayi da gahawa ke yi kamar shan taba sigari.

Ya ce ''Sinadarin caffeine ya dade a cikin nau'ika daban-daban da dan adam ke ci ko kuma sha''

" Kamar sauran sinadarai daban-daban da ake samu a irin na'ikan abincin yau da kullum, su kan iya zama hadari ga mata masu ciki muddin aka samu adadin su na da yawa a cikin.''

"Don haka, yanayin tattara bayanan wannna bincike da kusan a ce bangare daya ne, bai nuna cewa karancin sinadarin na caffein na da hadari ba, kana shawarar baya-bayan nan ta a guje wa caffein din ka iya sauya wa.