Harin Masallacin Christchurch: 'Na kusa yafe wa wanda ya kashe mijina'

Harin Masallacin Christchurch: 'Na kusa yafe wa wanda ya kashe mijina'

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mijin Hamimah Tuyan Zekeriya na ɗaya daga cikin mutum 51 da aka kashe a lokacin da aka kai hari wasu masallatai biyu a birnin Christchurch na ƙasar New Zealand a watan Maris ɗin 2019.

Ta je New Zeland daga Singapore domin ganin yadda shari'ar da ake yi wa maharin za ta kaya da kuma irin hukuncin da za a yanke masa.

A hirar da aka yi da ita ta ce ta kusa yafe wa wanda ya kai harin amma ba ta sani ba ko za ta yi hakan.