Harry Maguire: An cire dan wasan daga tawagar Ingila

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

Kocin tawagar kwallon kafar Ingila Gareth Southgate ya cire dan wasan Manchester United Harry Maguire daga tawagar kasar bayan an same shi da laifi a tsibirin Syros da ke Girka.

Ranar Talata Southgate ya sanya Maguire, mai shekara 27, a cikin tawagar Ingila a yayin da ake gudanar da shari'a a kansa.

An same shi da laifin cin zarafi, da kin yarda a kama shi da kuma yunkurin bayar da cin hanci.

Southgate ya ce an cire sunan Maguire ne "saboda yin hakan fa'ida ce ga dukkan bangarorin".

An yanke hukuncin daurin wata 21 da kwana 10 kan Maguire, ko da yake za a jira zuwa shekara uku, bayan ya yi fada a Mykonos.

Bayan yanke hukuncin, ya ce ya shaida wa lauyoyinsa nan take su gaya wa kotu cewa zai daukaka kara.

"Ina da kwarin gwiwar cewa ba ni da laifi a kan wannan batu - hasalima ni da iyalina da abokaina aka yi wa laifi" a cewarsa.

Da yake jawabi bayan fitar da jerin 'yan wasan da ke tawagarsa da za ta fafata a gasar Nations League da Iceland da kuma Denmark a watan gobe, Southgate ya ce ya yi magana da Maguire kuma "babu abin da zai sa na yi shakka kan abubuwan da ya gaya min".

A game da cire Maguire daga tawagarsa awa biyar bayan ya sanya shi, Southgate ya ce: "Kamar yadda na fada tun da farko a yau, ina iya sauya duk matakin da na dauka."

Sauran 'yan wasan da ke tawagar

Southgate ya bayyana 'yan wasan da ke tawagarsa cikinsu har da dan wasan tsakiyar Manchester City Phil Foden, dan wasan gaban Manchester United Mason Greenwood da kuma dan wasan tsakiyar Leeds Kalvin Phillips.

Sai kuma dan wasan gaba Danny Ings da gola Dean Henderson.

Kazalika akwai dan wasan Southampton Ings, da Jamie Vardy, da Harry Kane duk da killace shi da aka yi bayan balaguron da ya yi zuwa Bahamas.

Sai dai ba a sanya Jack Grealish ba.

Raheem Sterling da Kyle Walker na cikin tawagar ta Southgate.