Zaben Amurka na 2020: Melania Trump ta bukaci fahimtar juna kan bambamcin launin fata

Mai dakin shugaban Amurka Donald Trump wato Melania Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mai dakin shugaban Amurka Donald Trump wato Melania Trump

Matar shugaban kasar, Amurka Melania Trump ta yi tsokaci mai sosa rai kan batun hada kai game da wariyar launin fata a lokacin jawabinta daga fadar White House a yayin babban taron jam'iyyar Republican.

"A daina rikici da sace kayan jama'a," kiranta Kenan ga masu zanga-zanga a kan harbin da wani dan sanda ya yi a Wisconsin.

Ta bukaci Amurkawa su daina yin hasashe kan batun wariyar launin fata tayin la'akari da tarihin kasar.

A yanzu haka dai dan takarar Demokrat, Joe Biden shi ne kan gaba a kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a inda ya baiwa shugaba Donald Trump tazara.

Sai dai matakin da ta dauka na yin jawabi daga fadar mulkin kasar ya harzuka wasu 'yan jam'iyyar Democrat da ke cewa hakan ya saba ka'ida duba da cewa fadar shugaban kasa ta jama'a ce ba ta wani mutum ba.

Sauran wadanda suka yi jawabi a yayin taron sun hadar da sanata daga jihar Kentucky Rand Paul, wanda ya jinjina wa shugaba Trump saboda''Namijin kokarin da yace ya yi wajen farfado da kimar Amurka a idon duniya.

Me 'ya'yan Trump suka ce ?

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Saura kwana daya a kammala taron

'Ya'yan shugaba Trump da dama sun yi jawabi yayin taron, kuma yawancinsu, sun shaidi mahaifinsu a kan cewa mutumin kirki ne.

Eric Trump, ya yi kakkausar suka a kan yan jam'iyyar Democrat da ya kira ''Masu neman gurgunta kasar".

''Suna son su zubar da darajar taken kasarmu ta hanyar dukawa'' in ji shi, yayin da sojojin mu ke sadaukar da rayuwarsu a fagen daga domin kare 'yancinmu.

Ita kuwa Tiffani Trump da Ivanka Trump, sun zargi kafafen watsa labarai da sauya tunanin Amurkawa.

''Jawaban karya da kafafen watsa labarai ke bawa jama'a ya sauya musu tunani'' in ji su, ya kuma haifar da fargaba da rarrabuwar kai a tsakanin jama'a.

Saura kwana daya a kammala taron, in da a karshe shugaba Trump da mataimakinsa Mike Pence za su gabatar da jawabi a kan manufofinsu na shekaru hudu nan gaba idan suka samu nasara.