Za a fara yakin neman zabe a Tanzania

Shugaba John Magufuli
Bayanan hoto,

Shugaba John Magufuli

Za a fara yakin neman zaben shugaban kasa a Tanzania, gabanin babban zaben shugaban kasa da za a yi a karshen watan Oktoba.

Shugaba John Magufuli, wanda ke neman sake tsayawa takara, na fafatawa da mutane goma sha hudu da ke kalubalantarsa.

Masu sharhi sun ce mutane da dama na kallon shugaban wanda ya dare mulki shekaru biyar da suka gabata a matsayin mai kawo sauyi.

Ana sa ran samun dandazon mutane da zasu halarci yakin neman zaben da zai fara daga yau.

Sai dai tun bayan zuwansa, wasu na kallon shi a matsayin mai amfani da karfin da ya wuce kima wajen matsawa yan hamayya.

A watan Yuni ne ya bayyana kawo karshen cutar korona a Tanzania, sai dai ya ce an yi hakan ne da karfin addu'a.