An dakatar da mai unguwar da ake zargi da sayar da jariri a Kano

Jami'an hukumar Hisbah ta Kano

Asalin hoton, Getty Images

Masarautar Kano ta dakatar da mai unguwar Sabon Gari mallam Ya'u Muhammad, bayan da aka zarge shi da hannu a sayar da wani yaro mai shekara daya.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da masarautar ta Kano ta fitar a daren Talata daga ofishin Galadiman Kano kuma babban dan Majalisar sarkin na Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Ana dai zagin mai unguwar Malam Ya'u tare da shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar Fagge Jamilu Yusuf da sayar da wani jariri ga wata mata kan kudi naira dubu 20.

Mataimakin sakataren masarautar Awaisu Abbas Sanusi, ya shaida wa BBC cewa, an dakatar da mai unguwa Ya'u ne bayan rahoton da hakimin Fagge Alhaji Mamuda Ado Bayero ya gabatar a gaban sarki Kano.

An dai dakatar da mai unguwar ne har sai hukumomi sun kammala bincike.

Matashiya

Tun da farko dai hukumar da ke yaƙi da fatauci tare da bautar da al'umma ta NAPTIP a Najeriya shiyyar Kano ce ta bayyana cewa ta kama shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano da ke arewacin ƙasar bisa zargin siyarwa da wata mata wani yaro.

Shugaban hukumar ta NAPTIP shiyyar Kano, Shehu Umar ya shaida wa BBC cewar sun gayyaci shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Fagge, da mai unguwar sabon Gari, bisa zargin siyarwa da wata mata Misis Loveth Jamilu yaron da ta tafi da shi jihar Imo bayan basu naira dubu 20.

To sai dai kuma hukumar ta Hisbah ta ƙaryata rahoton cewa shugaban hukumar na Fagge ne ya sayar da yaron.

A yanzu haka dai an samu wanda suka ce suna so za su karɓi wannan yaro su ci gaba da kulawa da shi.

"Mai unguwar Sabon Gari shi ya yar da cewa za a miƙa wannan yaron hannun Jamila Kabir, wata mata haifaffiyar nan (Kano) aka yi yarjejeniya tsakanin kwamandanmu da mai unguwa da ita Jamila Kabir amma duk wata ɗaya za a dawo da shi mu riƙa ganin halin da yake ciki wanda da ma ita ce doka." in ji Ibn Sina.