Musa 'Yar adua: Mahaifina yana matuƙar son cin ƙosai da biredi

'Yar Adua

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Umar Musa Yar Adua ya yi mulkin Najeriya tsakanin 2007 zuwa 2010

Tsohon shugaban Najeriya marigayi Umar Musa 'Yar Adua yana matukar sha'awar cin kosai da kuma biredi da miya, a cewar dansa, Musa Yar Adua.

Musa ya bayyana haka ne a tattaunawa ta musamman ta shafin Instagram da Sashen Hausa na BBC kai-tsaye ranar Talata da almuru.

"Mahaifina yana son kosai amma da sanyi, kuma sai can tsakar dare, sannan yana son biredi da miya. Shi mutum ne wanda tsakani da Allah yana da saukin kai. Ko a cikin gidanmu gaskiya ba wanda ya biyo wannan hali ta wannan fannin...zai dawo daga aiki ya ci kosai hankalinsa ya kwanta', in ji Musa Yar Adua.

Ya kara da cewa yana matukar farin ciki game da yadda 'yan Najeriya suke yaba wa mahaifinsa saboda ayyukan da ya yi wa kasar, yana mai cewa "hakan na nufin duk abin da mutum zai yi ya kamata ya zama mutumin kirki."

Musa Yar Adua ya ce yana alfahari da kasancewa daga zuriyar da ta yi wa Najeriya hidima musamman ganin cewa kakansa, Musa Yar Adua, ya taba zama minista a gwamnatin farar hula ta farko, sannan kawunsa Shehu Yar Adua ya zama mataimakin shugaban kasa kuma mahaifinsa ya zama shugaban kasa.

Ya ce babban burinsa shi ne ya tabbtar bai bata sunan zuriyarsu ba musamman kan rawar da suka taka wajen cigaban Najeriya.

Sai dai Musa Yar Aduwa ya kara da cewa ba shi da niyyar shiga harkokin siyasa, ko da yake a shirye yake ya bayar da tasa gudummawar wajen cigaban Najeriya.

Waiwaye

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An haifi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a garin Katsina.

Mahaifinsa tsohon ministan Lagas ne a jamhuriya ta daya kuma matawallen Katsina, sarautar da marigayi Alhaji Umaru Musa Yar Adua ya gada.

Ya shiga makarantar firamare ta Rafukka a shekarar 1958, kuma daga bisani aka mayar da shi makarantar firamare ta kwana da ke Dutsimma.

A shekarar 1965 zuwa 1969 ya yi kwalejin gwamnati ta Keffi.

Daga nan kuma ya tafi kwalejin Barewa, inda ya kammala a shekarar 1971.

Ya shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1972 zuwa 1975, inda ya yi karatun digirinsa a fannin ilimin koyarwa da na kimiyyar sinadirai.

A shekarar 1978 ne ya koma jami'ar Ahmadu Bellon domin yin digirinsa na biyu a fannin ilimin kimiyyar sinadaren.

'Yar Adua ya sake tsayawa takarar gwamnan Jihar Katsina a shekarar 1999 karkashin tutar jam'iyyar PDP, inda ya yi nasara, an sake zabar sa a shekara ta 2003.

Alhaji Umaru Musa Yar Adua ya kasance gwamna da kuma shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa, a wani mataki da wasu ke ganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

Allah Ya yi wa Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua rasuwa ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2010, ya bar mace daya - Hajiya Turai Yar Adua - da 'ya'ya bakwai, biyar mata biyu maza.

Karin labarai da za ku so ku karanta: