Kisan kai a Afirka Ta Kudu: Ana zaman zulumi bayan gano gawarwakin wasu mata

A sugar cane field with a cross of one of the murdered victims superimposed on it and a woman praying at the site - Mthwalume, South Africa

Mutanen wani gari da ke noman rake a Afrika Ta Kudu na cikin tashin hankali bayan an ga gawarwakin wasu mata biyar da ke tsakanin shekaru 15 zuwa 38 jibge a wata gona, kamar yadda wakiliyar BBC Kyla Herrmannsen ta ruwaito.

'Yan uwa da abokan arziki na Zama Chiliza, na cikin yanayi na juyayi, inda Zama na daga cikin matan da aka ga gawarwakin su.

An shimfiɗe kayan sawarta wanda suka haɗa da riga da siket kan wata katifa, wanda hakan al'ada ce ta nuna juyayi ga wanda ya mutu.

An saka kendir kusa da inda ta ke kwantar da kanta a katifa - wanda hakan ke alamta kasancewar ruhinta. Kendir ɗin zai ta ci a kullum har sai an binne ta.

Zama, mai shekaru 38 ta ɓata tun a ranar 6 ga watan Yuli, ganinta na ƙarshe da aka yi shi ne aka ga ta fita daga wani babban kanti a Mthwalume, wani ƙauye da ke da nisan kilomita 90 daga garin Durban a lardin KwaZulu.

"Muna ta tunanin wani abin takaici zai faru, a kullum idan mun wayi gari, har muna tunanin da wuya idan za ta dawo da ranta," in ji wani ɗan uwanta Musawakhe Khambule, bayan 'yan sanda sun yi bincike ba su gano ta ba a farko.

Sai dai fargabar da 'yan uwanta ke yi ta tabbata a ranar 11 ga watan Agusta- makonni biyar bayan ta ɓata - inda wasu masu ɗaukar itace a gona suka yi kiciɓis da gawarta, a cikin wata gonar rake da ba a nomawa a gefen gari.

Tafiya kaɗan cikin dajin, mutum zai isa inda aka jibge gawar Misis Chiliza - ganyaryakin da aka yi amfani da su wurin luluɓe gawarta na nan a wurin.

"Gawarta ta fara ruɓewa, amma an gano ko ita wacece daga takardunta," in ji Khambule.

Ya bayyana ta a matsayin mace mai dattaku - ba irin matar da za ta jefa kanta cikin rigima ba ce, sakamakon ta mayar da hankali ne wurin kula da 'yarta mai shekaru 15.

"Mata ce mai son iyalinta, tana son 'yarta sosai, tana son tarayya da ita," in ji Mista Khambule.

'Yan uwar Misis Zama suna da labarin cewa an gano gawarwaki a yankin kwanakin baya, amma ba su taɓa kawo wa ransu cewa irin wannan lamarin zai faru da ita ba.

"Irin waɗannan mace-macen sun fara ne tun Zama na da rai. Muna jin labarin irin waɗannan kashe-kashen. Sai da ta kai wani mataki har sai da muka tattauna irin waɗannan kashe-kashen da ake yi tare da Zama inda muka bayyana ra'ayoyin mu a kai," In ji Mista Khambule.

"Mun shiga damuwa bayan ta ɓace," in ji shi: "Mun tashi rana ɗaya kawai muka ji labarin Zama ta mutu."

Kai wa mata hari a Afrika Ta Kudu

Afrika Ta Kudu na daga cikin ƙasashen da aka fi aikata laifuka a faɗin duniya - a shekarar da ta gabata, Shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa ƙasar na daga cikin wuraren da suka fi zama "barazana ga mata a duniya".

Duk da raguwar da aka samu na aikata laifuka a watannin farko na saka dokar kulle a ƙasar, yanzu an ci gaba da samun ƙazaman laifuka da ake aikatawa a ƙasar.

Gawar Chiliza, ita ce ta huɗu da aka gano a ƙauyen Mthwalume tsakanin watan Afrilu zuwa Agusta, wanda hakan ya sa 'yan sanda suke zargin akwai mai kashe mutane a yankin - sai 'yan sanda suka ci gaba da bincike a dajin.

Da taimakon karnukan 'yan sanda, an gano gawar wata mata da ta ruɓe washe gari a wannan gona, mallakar Siyabonga Gasa.

Mista Gasa ya bayyana cewa an daddatsa gawar. Sai dai 'yan sandan ba su bayar da shaidar cewa ko an ci zarafin matan da aka kashe ba ta hanyar fyaɗe.

An gano gawarwakin uku ne a gonarsa, biyu kuma a gonar makwafcinsa.

A halin yanzu dai 'yan sanda sun zagaye gonakin da igiya, da katako da wasu filawoyi. Matan yankin na ci gaba da zuwa wurin da lamarin ya faru domin gudanar da addu'o'i da waƙe-waƙe.