Zuri'ar gwaggon birin da ya kusa ƙarewa a duniya 'na ta hayayyafa' a Uganda

Gorilla and baby

Asalin hoton, Uganda Wildlife Authority

Bayanan hoto,

Ruterana ce gwaggon biri da ta haihu a baya-bayan nan a Bwindi

An haifi gwaggon birai biyar a cikin mako shida a Gandun Namun Daji na Bwindi, inda Hukumar Kula da Namun Daji ta Uganda UWS ta ayyana hakan a matsayin hayayyafa da ba a saba gani ba.

Da take sanar da haihuwar ta baya-bayan nan, hukumar UWS ta ce: "Iyalan gwaggon biri ta Rushegura na murnar samun karuwar jaririn gwaggon biri".

Jarirai bakwai aka haifa tun daga watan Janairun 2020 ba kamar na yadda aka samu a baki dayan shekarar 2019 ba da aka haifi uku kawai, a cewar UWS.

Ana samun raguwar gwaggon birai da ke rayuwa a tsaunuka inda a yanzu haka guda 1,000 kawai suke raye a doron kasa.

Hukumar UWS ta shaida wa BBC cewa wannan shekarar an ga abin da ba a saba gani ba na haihuwar gwaggon birai amma ba a gane dalilin da ya jawo wannan hayayyafa ba.

Haihuwa biyar din ta baya-bayan nan an yi ta ne daga iyalan birai daban-daban.

Wakiliyar BBC Afrika Catherine Byaruhanga ta ce karuwar hayayyafa na zuwa ne a yayin da gandun dajin ke hana zuwa ziyara wajen dabbobin sakamakon annobar cutar korona.

Za ku so ku karanta wannan...

An rufe mafi yawan bangarorin yawon bude ido na Uganda a watan Maris, amma a yanzu ana ta sake bude su, sai dai ana mayar da hankali sosai kan birai saboda kwayoyin halittarsu sun yi kama sosai da na dan adam.

A yanzu ana barin masu ziyara kadan suna shiga yankin da aka kare din bayan da aka samar da sabbin matakan kariya, kamar sanya takunkumi da bayar da tazara.

Farautar dabbobi na daga cikin manyan abin da ya dami hukumomi musamman a lokacin nan na kullen hana yaduwar cutar korona.

A watan Yuli, an yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 11 a gidan yari saboda kashe Rafiki, wani gwaggon biri mai baya launin ruwan gwal a Bwindi.

Akwai gwaggon birai kusan 400 a Gandun Daji na Bwindi da suka fito daga rukunin iyalai 10.

An fi samun wadannan gwaggon birai da suka fi zama a tsaunuka a yankunan da ake hana shiga a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo da Rwanda da kuma Uganda.

Baya ga Gandun Daji na Bwindi, ana kuma samun su a tsaunukan da ke Gandun Daji Virunga Massif da ke tsakanin iyakokin kasashen uku.

A shekarar 2018 hukumar kula da muhalli da dabbobi ta duniya IUCN, ta cire gwaggon birai na ''mountain gorillas'' daga jerin sunayen dabbobin da ke barazanar karewa a duniya, bayan da kwalliya ta biya kudin sabulu a kokarin da ta yi na yaki da farautarsu.

Amma a yanzu IUCN ta sake sanya nau'in dabbar a cikin jerin dabbobin da ke barazanar karewa.