Gubar Novichok aka sanya wa jagoran adawa na Rasha Navalny - Gwamnatin Jamus

Navalny

Asalin hoton, Reuters

Gwamnatin Jamus ta ce gubar Novichok aka sanya wa jagoran adawa na Rasha Alexei Navalny.

Ta ce wani gwaji da aka yi ya gano ''tabbas hakika'' gubar Novichok ce a jikinsa.

A watan da ya gabata ne aka garzaya da Mr Navalny birnin Berlin na Jamus don a yi masa magani bayan da ya fara rashin lafiya a yayin da yake tafiya a cikin jirgi zuwa yankin Siberia na kasar Rasha.

Tun a lokacin ya yi dogon suma bai farfado ba.

Tawagarsa ta ce guba aka sanya masa a bisa umarnin Shugaba Vladimir Putin. Amma Fadar Kremlin ta yi watsi da zargin.

Gwamnatin Jamus ta ce ta yi Allah-wadai da harin da babbar murya ta kuma yi kira ga Rasha da ta yi gaggawar yin bayani.

"Abun daga hankali ne cewa an sanya wa Alexei Navalny guba a Rasha,'' in ji ta.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da manyan ministocinta don tattaunawa kan matakai na gaba, a cewar sanarwar gwamnatin.

Fadar Kremlin ta Rasha ta ce ba ta samu kowane irin bayani daga Jamus cewa gubar Novichok aka sanya Mista Nevelny ba, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar na Tass.

Amma likitocin da suka duba shi a Rasha sun ce ba su ga alamar guba a jikinsa ba.

Mr Navalny ya fara rashin lafiya ne a cikin jirgi a Rasha ranar Alhamis.

Wani bidiyo da ya bayyana ya nuna Mr Mr Navalny, mai yawan sukar gwamnatin Rasha, yana murkususun ciwo a cikin jirgin mai zuwa Moscow daga birnin Tomsk na Siberia.

Nan da nan aka yi saukar gaggawa a Omsk inda aka fara duba shi.

Magoya bayansa sun yi zargin guba aka sanya masa a kan kofin shayin da ya sha a filin jirgin saman Tomsk.

A wata sanarwarsu ta baya-bayan nan bayan ta tawagar likitocin Jamus, likitocin Omsk sun ce gwaji bai nuna alamar guba a jikinsa ba.

A makon d ya gabata tawagar ta ce watakila wani ciwo ne mai alaka da yin kasa da sikarin jikinsa ya yi.

A ranar Juma'a, sun ce yana cikin yanayi mai tsanani da ba za a iya tafiya da shi ba, amma daga baya aka sanya shi a jirgin gaggawa, inda ya sauke shi a Berlin a ranar Asabar da safe.

Me likitocin Jamus suka ce?

Sanarwa daga Jamus din ta ce yana cikin ''yanayi mai tsanani amma ba ya cikin barazanar rasa ransa.''