Yahaya Aminu Sharif: Wanda ya yi wa Annabi SAW batanci a Kano ya daukaka kara

Aminu

Asalin hoton, Idris Ibrahim

Matashin nan da wata Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta yankewa hukuncin kisa a Kano bisa samun sa da laifin batanci ga Annabi Muhammadu SAW, ya daukaka kara zuwa babbar kotun jihar yana kalubalantar hukuncin da aka yanke masa.

A ranar Alhamis din nan ne matashin ya daukaka karar kwanaki kadan gabanin cikar wa'adin da kotun da ta yanke hukuncin ta ba shi.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar wa da BBC cewa lauyoyin Yahaya Shariff Aminu sun ba da sanarwar daukaka kara.

"Hakan na nufin cewa ya tsallake siradin zartar masa da hukunci matukar ya wuce kwana 30 bai daukaka kara ba kan hukuncin da aka yanke masa", in ji Baba Jibo.

A ranar Laraba shahararren lauyan nan mai kare hakkin bil adama Cif Femi Falana ya yi zargin cewa kotun ta Kano ta hana takardun shari'ar, wadanda za su ba da damar daukaka kara, duk da shafe kusan mako biyu ana neman takardun shari'ar.

To sai dai Baba Jibo ya musanta zargin, inda ya ce a ranar Talata ne kawai ake nemi kwafin hukuncin, kuma aka bai wa lauyoyin Yahaya din ranar Laraba.

Kakakin kotunan na Kano ya ce sai nan gaba ne babbar kotun za ta zabi alkalai biyu ko uku da za su saurari daukaka karar.

Dalilan daukaka karar

A bayanan da suka gabatarwa kotun, masu daukaka karar sun bayyana dalilansu na daukaka karar, to sai dai Baba Jibo ya ce ba zai bayyana dalilan ba har sai masu shigar da karar sun bayyana su a gaban kotu.

"Sun shigar da karar ne suna kalubalantar gwamnan Kano da kuma kwamishinan shari'a na jihar, kan hukuncin da aka yanke", a cewar Baba Jibo.

A yanzu Kotun Daukaka Karar za ta yi amfani ne da Kundin Hukunta Laifuka na Kano na shekarar 2019 yayin shari'ar.

Sai dai har kawo yanzu ba a tantance ranar da za a fara sauraron dauka karar ba.

"Ya danganta da irin yawan kararrakin da suke kan layi," a cewar Baba Jibo.

"To amma ina tabbatar maka tun da sun riga sun ba da sanarwar daukaka kara, ba za a dauki wani lokaci ba, za a sanya ranar da za a gabatar da ita, kana kuma a fara sauraronta."

Me ya faru a ranar Laraba?

A ranar Laraba jaridar Punch ta yi zargin cewa Kotun Shari'a ta hana Aminu Yahaya Sharif damarsa ta daukaka kara, wacce za ta kare ranar 10 ga watan Satumba.

Amma mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya karyata zargin, yana mai cewa sai jiya (ranar Talata) aka tuntube su da son su ba da kwafin shari'ar don daukaka kara.

Me Cif Falana ya ce?

Wani babban lauyan kare hakkin dan adam a Najeriya, Cif Femi Falana- SAN ya shaida wa BBC cewa tun mako biyu da suka gabata yake tura dan aike Kotun Shari'ar Musuluncin ta Kano domin karbo kwafin shari'ar da za a yi amfani da shi wajen kai batun Kotun Daukaka Kara.

Asalin hoton, Femi Falana/Facebook

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

''Ko a ranar Talata ma na aika mutum amma kememe suka ce mana babu kwafin shari'ar, to ai ku 'yan jarida ne ku tambaye su su aiko muku da kwafin ku gani mana,'' in ji Mista Falana.

Sai dai BBC ta tuntubi Baba Jibo Ibrahim wanda ya ce a ranar Talata ne kawai wani lauya ya je musu don neman kwafin shari'a da nufin daukaka kara, ''babu wanda ya tuntube tun mako biyu da suka wuce.''

''A ranar Talata ne, kuma da ya je mun gaya masa ana shirya kwafin a kumfuta tare da tacewa, mun ce za a aika masa ranar Alhamis bayan na shigar da rubutun Larabci ciki.

''Za a yi kwafi uku, daya nawa, daya na atoni janar na jiha, daya kuma na shi lauyan da ya nema,'' in ji Baba Jibo.

Binciken da BBC ta yi ya nuna cewa Aminu Sharif, wanda har yanzu yake tsare a gidan yari ba shi da wani lauya mai tsaya masa kan shari'ar.

Amma Mista Falana ya tabbatar mana da cewa bayan da ya ga lokaci na kurewa sai ya nemi shiga lamarin, ''sai na ga ashe ma ba shi da mai tsaya masa, to shi ne nake ta aike don a samo kwafin shari'ar mu daukaka karar amma abu ya faskara.''.

Babban lauyan ya ce a yanzu ya shiga cikin maganar dumu-dumu kuma ba zai hakura ba har sai ya samu kwafin shari'ar sannan ya tuntubi hukumar lauyoyi ta kasa don samar wa Yahaya lauyan da zai kare shi a kotu ta gaba.

Ya kuma ce ya yi ta kokarin ganin an ba su damar gana wa da Yahaya Sharif amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Me ya faru tun farko?

A watan da ya gabata ne Kotun Shari'ar Musulunci ta yanke wa Aminu Sharif hukuncin kisa bayan samun sa da laifin yi wa Annabi Muhammad SAW batanci a wata waka da ya yi a bara.

Sai dai kotun ta ba shi damar daukaka kara zuwa kotu ta gaba idan har hukuncin bai yi masa ba, kuma ko da Kotun Daukaka kara da ta Koli sun ta tabbatar da hukuncin, to dole sai gwamnan jihar Kano ya sanya hannu kafin a aiwatar da hukuncin kisan a kan Aminu Yahaya Sharif.

To amma a makon da ya wuce gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu kan aiwatar da hukuncin kisan da idan har bai ɗaukaka kara ba.