Nuna mana aikin da ka yi wa arewacin Najeriya – 'Yan Twitter ga Buhari

...

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Matasa da dama 'yan arewacin Najeriya sun harzuƙa a shafukan sada zumunta musamman Tuwita inda suke ta tambayoyi da amayar da abin da ke cikinsu kan gwamnatin Shugaba Buhari.

Da alama wasu 'yan ƙasar ba su gamsu da kamun ludayin gwamnatin ƙasar ba ne shi yasa suke caccakar mulkin shugaban.

'Yan ƙasar musamman waɗanda suka fito daga arewaci suna amfani da maudu'in #NorthernProjects, inda suka kafe kan cewa kusan dukkan ayyukan da shugaban ƙasar ya yi alƙawarin zai yi bai cika su ba.

Sakamakon harzuƙar da wasu 'yan ƙasar suka yi, har suna cewa gwara gwamnatin jiya da ta yau a ƙasar.

Ga dai wasu daga cikin sakonnin da mutane ke wallafa a tuwita din a ranar Laraba.

@Realoilsheikh tambaya yake yi kan inda aka kwana kan batun samar da wutar lantarki ta Mambilla, da kuma batun tashar jirgin ruwa ta Baro a jihar Neja?

Ya kuma yi tambaya kan batun hanyar Kano zuwa Maiduguri da kuma inda aka kwana kan batun hanyar Abuja zuwa Kaduna da gwamnatin ƙasar ta yi alkwarin yi.

Wasu daga cikin masu caccakar gwamnatin shugaban ƙasar, suna zarginsa da cewa ya fi mayar da hankali wurin yin ayyuka a kudancin ƙasar fiye da arewaci.

Wannan kuma cewa ya yi a lokacin da Shugaba Buhari ke neman shugabanci, ya yi alƙawura da dama da hakan ya sa mutane suka yi amfani da kuɗinsu da karfinsu suka zaɓe shi domin ya hau mulki.

A yanzu da ya hau mulki, ya gaza cika alƙawuran da ya yi wa 'yan Najeriyar.

Wannan kuma ya yi iƙirarin cewa ya sadaukar da motarsa yayin yaƙin neman zaɓen Buhari sakamakon yana tunanin idan Buhari ya samu mulki zai zuba wa arewacin Najeriya ayyuka ba tare da sanin cewa ba haka abin yake ba.

A cewarsa, a yanzu dai shugaban yana gasa su.

Sai dai duk da cewar masu sukar shugaban sun fi yawa, amma kamar yadda Bahaushe ya ce ba a rasa nono a riga, to haka ma akwai 'yan tsiraru da suke kare shi.

Wani Sarki @Wassapin ya ce: ''Idan da za a iya waiwayen baya, to da Shugaba Buhari zan sake zaba a kan Goodluck Jonathan da ya gaza a wancan lokacin.

Ba zan taba da-na-sanin zabar Buhari ba don kawai ya gaza. Abin da na yi shi ne daidai.''

Lawal Abdullahi Giza ma cewa ya yi: Gwarzo, mai kishin kasa, mai gaskiya, Allah Ya yi maka albarka Buhari.

''Kuna da damar dana sanin zabarsa amma ni kam ba na da na sani.''

Irin waɗannan abubuwan dai ake ta tattaunawa a Twitter da maudu'in #NorthernProjects, inda da dama suna ta ƙorafi kan matsalar tsaro da tattalin arziƙi.u

Ba wannan ne karon farko da 'yan ƙasar ke caccakar shugaban a shafukan sada zumunta ba, ko a ranar 17 ga watan Agusta ma masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriyar sun kirkiri maudu'in #ThankyouBuhari inda suka dinga yi wa shugaban shagube kan ''gazarwarsa'' da sunan suna masa godiya.

Sannan kwanakin baya ma har sai da aka gudanar da zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya kan kashe-kashen da ake yi da kuma tattauna maudu'in #NorthernLivesMatter a shafukan sada zumunta.

Baya ga wannan maudu'i na ranar Laraba #NorthernProjects, 'yan Tuwitar kuma sun sake ƙirkirar wasu maudu'an na #Buhari wanda aka yi amfani da shi sau fiye da 42,000 da #SaiBaba wanda aka yi amfani dab shi sau fiye da 2,500 inda suke koka wa kan ƙkarin farashin man fetur din da gwamnati ta yi a ranar zuwa N151.56k duk lita daya.

Sun kuma yi ta kokawa kan yadda farashin shinkafa ke tashin gwauron zabi a ƙasar.