Kashi 30 na 'yan Najeriya ba su da lafiyar ƙwaƙwalwa - Kwararru

lafiyar kwakwalwa
Bayanan hoto,

Wani al'amari da ake ganin ya taba lafiyar kwakwalwar mutane a baya-bayan nan shi ne annobar cutar korona wadda ta jefa al'ummar duniya a halin dimuwa da rashin tabbas

Kwararru a fannin lafiyar kwakwalwa a Najeriya na cewa jama'a da dama na da matsalolin kwakwalwar da ba su san suna da su ba wadanda ka iya kai wa ga hauka.

Mutane da dama na fama da larura a kwakwalwarsu amma ba tare da sun sani ba ko kuma sun san da matsalar amma sai su nuna ba ta faruwa.

Dr Auwal Abubakar Fatihu na fannin kula da masu tabin kwakwalwa a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano a Najeriya ya ce "ina mamakin yadda za ka jama'a na tururuwa zuwa ganin likita sakamakon samun larura a hantarsu ko koda ko ciki da ido da dai sauransu amma idan aka yi batun lafiyar kwakwalwa sai mutane su yi zaton komai kalau ba tare da sun je wurin likita ba."

Hakan ne ya sa "wata kididdiga ta nuna cewa kashi 30 na masu zuwa asibiti a kowane gari a Najeriya na fama da matsalar kwakwalwa da ake kira psycological problems", in ji Dr Auwal.

A Najeriya da kasashen Afirka danganta mutum da samun rashin lafiyar kwakwalwa tamkar bayyana mutum da mahaukaci ne inda a wasu lokuta irin wadannan furucin kan kai ga yin shari'a.

To sai dai likitocin kwakwalwa sun ce ba haka lamarin yake ba kasancewar idan za a yi zube-ban-kwaryata to da dama daga cikin mutane ba su da lafiyar kwakwalwa.

Alamomin larurar kwakwalwa

Kwararren kan fannin lafiyar kwakwalwa, Dr Auwalu Fatihu Abubakar ya zayyana wasu alamomi karkashin abin da ya kira sauye-sauye wajen yadda mutum yake gudanar da al'amuransa, a matsayin alamomin larurar kwakwalwa.

 • Rashin son shiga mutane
 • Rashin bacci
 • Rashin magana
 • Rashin tsaftar jiki
 • Yawan fada
 • Rashin hakuri
 • Alamar damuwa
 • Tunanin jama'a sun tsane shi.

Abubuwan da ke haddasa larurar kwakwalwa

 • Shiga yanayin kunci sakamakon zamantakewa a gida ko wurin aiki ko kuma kasuwa
 • Kunci ko matsi a rayuwa da ake kira ''Stress''
 • Sannan akwai yanayin mutum da ake kira 'personality' inda mai wannan halayya yake da saurin damuwa sakamakon wani abu.

Alakar larurar kwakwalwa da hauka

Dr Auwal ya ce alakar da ke tsakanin larurar kwakwalwa da ciwon hauka shi ne ciwon hauka cuta ce daya daga cikin larurorin kwakwalwa.

Sai dai masanin lafiyar kwakwalwar ya ce larurar kwakwalwa ka iya jefa mutum cikin yanayin hauka daga bisani.

"A kan samu yanayin da mutum musamman matasa a wannan zamanin kan samu kansu a yanayin damuwa da matsi da kuncin rayuwa, abin da ke sanya su su fada yanayin shaye-shaye domin samun mafita. Hakan daga bisani na sa su samu ciwon hauka."

Dangane da abubuwan da suke sanya hauka, Dr Auwalu ya ce "akwai dalilai masu yawa da ke sanya mutum ya zama mahaukaci amma kuma ana gado daga dangi da ake kira 'familial factor' sannan kuma ana samun hauka ta hanyar kaddara.

Ana kuma samun hauka sakamakon matsi na rayuwa da shaye-shaye da kuma sakamakon buguwa yayin wani hatsari."

Mafita

Hanyoyin magance matsalolin kwakwalwa musamman wadanda ba ciwon hauka ba ne su ne guda biyu:

 • Sauya tsarin rayuwa wato idan mutum yana da daukar al'amura da zafi to ya yi wa kansa fada domin ganin yadda zai sassauta
 • Tuntubar likitoci domin samun shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar kafin ta ta'zzarax.

Wani al'amari da ake ganin ya taba lafiyar kwakwalwar mutane a baya-bayan nan shi ne annobar cutar korona wadda ta jefa al'ummar duniya a halin dimuwa da rashin tabbas.

A kasashen Turai da wadanda suka ci gaba, jama'a sun yi ta tururuwa zuwa wurin likitocin kwakwalwa domin duba lafiyar kwakwalwar tasu baya ga rubuce-rubuce da masana suka yi ta yi kan yadda al'umma kan yadda za su kare kansu daga fadawa yanayin samun tabin kwakwalwa.