Takaddama kan kogin Nilu: Amurka za ta zaftare $100m daga tallafin da take bai wa Habasha

Madatsar ruwan za ta kasance mafi girma da ke samar da wutar lantarki a Afrika,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Madatsar ruwan za ta kasance mafi girma da ke samar da wutar lantarki a Afrika,

Rahotanni na cewa Amurka na shirin zaftare Dala Miliyan 100, kwatankwacin sama da Naira Biliyan 30 daga tallafin da take bawa Habasha sakamakon takaddama a kan samar da katafariyar madatsar ruwa a kogin Nilu.

Wata majiya daga gwamnatin kasar ta ce matakin na da alaka da gaban-kan da Habashan ta yi wajen soma makare madatsar ruwan tun kafin a kai ga cimma yarjejeniya da kasashen Masar da Sudan.

Masar ta jima tana adawa da shirin, wanda da zai rage yawan ruwan da take samu.

Ita kuwa Habasha ta jaddada cewa tana son samar da madatsar ruwan ne domin karfafa wutar lantarkinta.

Da zarar an kammala aikin samar da madatsar ruwan, za ta kasance mafi girma da ke samar da wutar lantarki a Afrika, sannan za ta rika bawa al'ummar kasar Miliyan 65 wuta.

Kudin da Amurkan ke shirin dakatar da bawa kasar na da nasaba da tallafin samar da abinci mai gina jiki, da tsaron yanki ko kan iyaka kamar yadda majiyar ta rawaito.

Sannan wani bangaren kudin ya shafi wanda ake bayarwa da zummar yaki da cutar Sida ko Kanjamau ta HIV da matsalar kwararar 'yan cirani da 'yan gudun hijira.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar ya fada wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, matakin da Habasha ta dauka na fara makare madatsar ruwan yayin da take tsaka da tattaunawa da kasashen Masar da Sudan, ya janyo nakasu ga tattaunawar da ake yi, sannan ya saba da ka'idojin da aka shimfida

Kalli yadda madatsar ruwan take a wannan bidiyon

Jakadan Habasha a Amurka ya shaida wa jaridar Financial Times cewa yana fatan Amurka za ta sauya tunaninta kan rage tallafin.

Fitsum Arega ya ce, "Mun nemi su sake tunani kuma muna jira. Muna fatan shekaru 117 na huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ba za su tashi a banza ba" in ji shi.

Masu aiko da rahotanni sun ce da alama za a kalli lamarin a matsayin wani mataki da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na hukunta Habasha, bayan kasar ta ki amincewa da sasantawar da Amurka ta yi da Masar da Sudan.

Tattaunawar ta tsaya kan batutuwa da dama da suka hada da bukatar da Masar da Sudan suka yi na cewa duk wata yarjejeniya ta kasance ta yi dai-dai da yadda za a gudanar da madatsar ruwan a lokutan fari.

Yankin da za a samar da madatsar na da kusanci da Masar kuma iskar wurin na da karfin sarrafa kwararar ruwan da kasar ke samu.

Kogin Nilu shi ne tushen ruwan sha da kuma noman rani ga kasar Masar.

Manoman kasar na girbin alkama a wani kauye da ake kira Shamma a lardin al-Minufiyah, kusa da kogin na Nilu.