Zaben Amurka na 2020: Trump ya bukaci masu zabe su kada kuri'a sau biyu

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci masu zabe a muhimmiyar jihar da ake kai ruwa rana a zaben shugaban kasar wato North Carolina da su kada kuri'a sau biyu yayin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

A hukumance, yin irin wannan zabe tamkar magudin zabe ne.

Yayin wata ziyara da ya kai jihar, Mista Trump ya ce bai gamsu da yadda yawancin al'ummar jihar suka amince su yi zabe ta hanyar aika kuri'unsu ta akwatun gidan waya ba.

A don haka ne ya bukaci masu zabe a jihar su kada kuri'a a ta hanyar da aka saba wato bin layin jefa kuri'a, ko da kuwa sun aika kuri'unsu ta akwatun aikawa da sakonnin gidan waya.

Yin zabe sau biyu dai babban laifi ne a dokokin Amurka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump na zargin aika kuri'a ta gidan waya na iya taimakawa abokin hamayyarsa Joe Biden.

Ya sha yin zargin cewa yin zabe ta akwatun gidan waya na iya haifar da magudi, yana cewa hakan zai amfani abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrat Joe Biden.

Masu suka na zargin shugaban kasar da kokarin kawo nakasu ga kwarin gwiwar da jama'a ke da shi a kan zaben.

Shugaba Trump da kwamitin yakin neman zabensa na ta hankoron ganin sun samu karbuwa a muhimman jihohin kasar da ke bawa dan takara damar lashe zaben shugaban kasa idan ya samu mafi rinjayen kuri'unsu

Shi dai dan takarar jam'iyyar Democrat Joe Biden ya ce ''Shugaba Trump ya saka Amurka cikin baƙin duhu na lokaci mai tsawo."

Watanni biyu da 'yan kwanaki suka rage a fafata a babban zaben shugaban kasar, kuma sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa Biden ne a kan gaba.