Makarantar NDA: Matakan da za ku bi don samun aiki a rundunar sojan Najeriya

Kwalejin horas da manyan sojoji ta NDA a Najeriya

Asalin hoton, @nda.edu.ng

Kwalejin horas da manyan sojoji ta NDA a Najeriya ta fitar da sunayen waɗanda suka ci jarrabawar karatun aikin soja tare da sanar da ranar da za a tantance su.

Sanarwar da Birgediya Janar Ayoola Aboaba, Rijistaran NDA ya fitar a ranar Laraba na ƙunshe da sunayen waɗanda suka ci jarrabar a dukkanin jihohin Najeriya 36 haɗi da Abuja.

Sanarwar ta ce za a fara tantance waɗanda suka ci jarrabawar ne daga ranar Asabar 12 ga watan Satumba zuwa 24 ga Oktoba a kwalejin da ke Kaduna.

Kuma an rarraba jihohin zuwa gida uku da kuma ranakun da za su halarci NDA domin tantance su.

Za a fara tantance kashi na farko na jihohin a ranar 12 ga watan Satumban 2020 kuma jihohin sun haɗa da: Anambra da Bauchi da Delta da Edo da Ekiti da Enugu da Gombe da Kano da Kaduna da Nasarawa da Ondo da kuma Filato.

Kashi na biyu na jihohin kuma za a tantance su ne a ranar 26 ga Satumba kuma sun haɗa da: Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Benue da Imo da Katsina da Kogi da Osun da Oyo da Rivers da Yobe da kuma Zamfara.

Kashi na uku na jihohin kuma za a tantance su ne a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba kuma sun haɗa da: Bayelsa da Borno da Cross River da Ebonyi da, Abuja da Jigawa da Kebbi da Kwara da Lagos da Neja da Ogun da Sokoto da kuma Taraba.

Sanarwar da NDA ta fitar ta ce babu wata dama ga duk wanda ya yi kuskuren halartar wurin tantacewar a ranakun da aka sanar.

Ga yadda za ku nemi shiga NDA

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

NDA makaranta ce ta gaba da sakandare kuma duk wanda zai shiga aikin makarantar ta soja sai ya kammala karatun sakandare kuma ya ci jarrabawar kammala sakandaren.

Kuma akwai adadin yawan ɗaliban da ake ƙayyadewa duk shekara, kamar a bana ɗalibai 80 aka kira daga kowacce jiha, yayin da aka kira ɗalibai 60 daga Abuja.

Kafin shiga NDA sai ɗalibi ya yi jarrabawar shiga manyan makarantu ta Jamb kuma ya saka NDA a matsayin zaɓinsa na farko.

Akwai kuma adadin makin da ake son ɗalibi ya samu a Jamb kafin shiga NDA. Ɗaliban fasaha da sadarwa da kuma tsaron Intanet da sauransu sai sun samu maki 210.

Ɗaliban kimiya da siyasa da tattalin arziki da sauran fannoni sai sun samu maki 180 a Jamb.

Waɗanda suka ci makin da ake buƙata za a kira su sake rubuta jarrabawar shiga NDA.

Idan ɗalibi ya ci jarrabawar za a kira a tantance shi a gaban kwamitin NDA. Za a tantance takardunsa na makaranta.

Za a kuma duba lafiyarsa da cancantarsa a kuma tabbatar da ba shi da wata nakasar jiki.

Idan ɗalibi ya tsallake matakin tantancewa, za a kira shi horo na musamman na guje-guje da tsalle-tsalle domin tabbatar da cancantarsa a aikin soja.

Idan ɗalibi ya tsallake matakin tsalle-tsalle da guje-guje zai kuma fuskanci wani kwamiti mataki na ƙarshe da za a zaɓi waɗanda suka fi ƙwazo.

Sauran abubuwan da ake buƙata

Asalin hoton, @nda.edu.ng

Ana son ɗalibi ya zo da kwafi biyu na takardunsa na makaranta da kuma takardar shaidarsa ta JAMB da ya rubuta.

Ana son ɗalibi ya zo da shaidar takardar fom da ya cike na NDA da kuma katin jarabawar tantancewa.

Takardun makaranta da ake son ɗalibi ya zo da su sun ƙunshi jarabawarsa WASSCE ko NECO da takardar shaidar kammala sakandare da Firamare.

Takardar shaidar haihuwa da takardar shaida daga ƙaramar hukumar inda ɗalibi ya fito mai ɗauke da sa hannun sakararen gwamnati ko kuma shugaban ƙaramar hukuma.

Sai ɗalibi ya samo takardar shaida daga wani soja wanda ya kai muƙamin Laftanal Kanal na sojan ƙasa ko sama, wanda za a iya amfani a madadin takardar shaidar ɗan kasa daga ƙaramar hukuma (Indigeneship)

Kuma sai jami'in sojan ya bayyana matsayinsa a wasikar da adireshinsa da numbar wayansa da kuma Imel. Sai kuma ya buga tambarinsa.

Kuma ɗalibi sai ya gabatar da fom da zai sauke a shafin intanet na NDA da iyayensa ko masu kula da shi za su cike kan amincewarsu da shiga aikin soja.

Duk dalibi da ya kasa kawo takardun da ake buƙata ba za a saurare shi ba kuma za a kore shi.

Duk wani Gyara da aka yi wa wata takarda zai kai ga korar ɗalibi.

Kayayyakin da ake son ɗalibi ya zo da su:

  • Kayan rubutu
  • Gajeren wando shuɗi guda uku da riga fara (T-shirts)
  • Takalmi fari Kanbas da safa farare guda uku
  • Kayan wanka soso da sabulu
  • Ɗalibi zai biya N2,500 na tabbatar da jarabawarsa ta WAEC/NECO
  • Katin diba jarabawar WAEC da NECO
  • Lambar BVN da lambar asusun banki
  • Hotunan fasfo guda hudu
  • Takunkumi