Farashin fetur a Najeriya: Me ake nufi da kasuwa ta yi halinta?

man fetur

Asalin hoton, Others

Hukumar da ke kayyade farashin man fetur ta Najeriya ta sanar da cewa yanzu gwamnati ta janye tallafin da take bayarwa a bangaren man fetur.

Saboda haka aikinta na kayyade farashin mai ya kare, kenan kasuwa ce za ta yi halinta.

Babbar jam`iyyar hamayyar kasar wato PDP, da kungiyoyin kwadago da na farar-hula da dama na sukar matakin.

Dakta Ahmed Adamu, kwararre ne a bangaren tattalin arzikin man fetur da ke koyarwa a jami`ar Nile da ke Abuja, kuma ya yi wa BBC bayani a kan abin da janye tallafin mai ya kunsa:

"Deregulation na nufin gwamnati ta cire hannunta daga cikin harkokin man fetur. Ma'ana gwamnati ta tsame hannunta daga cikin saye da sayarwa da kuma kayyade farashin da za a sayar da man fetur. Ta yadda ba gwamnati ce za ta kayyade farashin ba, kasuwa ce za ta iya tantance hakan. Kuma hakan na nufin babu wani tallafi da za ta bayar.

Kuma shi farashin danyen man fetur yana yawan hawa yana sauka, to idan gwamnati ta cire hannunta, yau za ka iya zuwa gidan mai ka tarar ana sayar da shi N150 amma gobe idan ka dawo za ka iya tarar da shi N170, ko kuma ya yi baya ya koma N140. Wato dai babu wani tsayayyen farashi. Kuma tana iya yiwuwa ya yi sama sosai musamman idan aka samu karancin danyen man fetur.

Ko kuma aka samu tsadar kudaden waje saboda wasu dalilai. Shi ya sa idan kasuwa za ta yi halinta babu, to ka ga babu maganar tallafin mai. Kuma a wannan lokaci da ake cikin tsananin wahala, gwamnati ta gwada cewa tana kashe makudan kudade wajen tallafin mai saboda ana yawan bukatar man.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai ina ganin ba wannan ne lokacin da ya dace a cire tallafin man ba saboda mutane suna cikin wahala. Lokaci ne da ya kamata a tallafawa mutane. Kuma idan har gwamnati za ta cire tallafi ya kamata a dauki wasu matakai. Idan ta gaza assasa matatun mai, bai kamata a cire tallafin man fetur ba saboda 'yan kasuwa za su iya hada kansu su sanya mai ya yi tsada kodayake gwamnati za ta sa ido a kansu.

A daidai wannan lokaci idan aka cire tallafi, farashin man fetur zai tashi sosai fiye da yadda yake duk da cewa yanzu farashin danyen man fetur bai yi sama ba sosai amma saboda wasu dalilai musamman saboda tashin dala. Don haka farashin da ake sayar da mai a gidajen mai zai tashi.

Sannan kuma bayan tashin da zai yi na farko, zai ci gaba da hawa yana sauka, ba za a taba samun daidaituwa na farashin ba saboda abubuwa guda biyu: farashin danyen man fetur a kasuwar duniya abu ne da yake hawa yana sauka; duk lokacin da ya hau a kasuwar kasashen duniya a nan ma zai tashi.

Idan ya sauka a can, a nan gidajen mai ma zai sauka. Sannan kuma hauhawar farashin dala yana tasiri a kan farashin danyen man fetur. Idan dala ta yi tsada man fetur a gidan mai zai yi tsada. Idan dala ta yi araha man fetur zai iya saukowa a gidan mai.

Sannan kuma farashin mai ya tashi sauran kayan masarufi za su tashi saboda mafi yawan abubuwan da ake samarwa suna dogara ne da farashin man fetur.

Ko da bai shafin farashin kai tsaye ba, za ka ga cewa wasu abubuwa sun tashi. Kuma idan man fetur ya yi tsada sannan kayayyaki suka yi tsada akwai masana'antun da za a iya rufewa saboda su ma sun dogara ne da farashin man fetur. Hakan zai sa a kori ma'aikata lamarin da zai haifar da rashin aikin yi da rashin tsaro.

Matashiya

A ranar Laraba 2 ga watan Satumbar 2020 ne ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci 'ya'yanta su ƙara kuɗin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

IPMAN ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.

Tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari karagar mulkin Najeriya, an yi ta samun ƙarin kudin man fetur a lokutan daban-daban, kamar dai yadda ya sha faruwa a gwamnatocin baya.

Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka taɓa yin ƙarin farashin mai a ƙasar ba, hakan ya tayar da hankalin mutane da dama.